GANGANCI: Dan shekara tara ya fada rijiya a Kano

0

Kakakin hukumar kashe gobara na jihar Kano Saidu Mohammed ya bayyana cewa wani yaro Haliru Abdullahi, mai shekaru tara ya fada rijiya.

Mohammed ya fadi haka ne ranar Litini dayake ganawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a garin Kano.

Ya ce wannan abin takaicin ya faru ne a kauyen Kofar Kudu dake karamar hukumar Gaya da karfe tara na safiyar Lahadi.

‘‘Mai Unguwar kauyen Hamza Abullahi ranar Lahadi da safe ya sanar da mu cewa Haliru ya fada wannan rijiya ne a dalilin wasan da ya je yi da abokanan sa a kusa da rijiyar.

‘‘Daga nan kuwa muka kokarin ceto wannan yaro amma hakan bai yiwu ba. Kafin a ciro shi ya riga mu gidan gaskiya.

A karshe Mohammed ya yi kira ga iyaye da su rika kula da walwalan ‘ya’yan su domin guje wa irin haka.

Share.

game da Author