GADAR ZARE: Yadda Ministan Shari’a Malami ya yi wa shari’ar naira biliyan 5.7 kafar-ungulu

0

Ministan Shari’a kuma Antoni Janar Abubakar Malami, ya yi wa wata shari’ar da ake yi wa wasu jami’an gwamnatin Katsina asarkala a Babbar Kotun Jihar Katsina.

Ana tuhumar tsoffin jami’an gwamnatin jihar Katsina a zamanin mulkin Gwamna Ibrahim Shema. Wadanda ake tuhumar din sun hada Nasiru Ingawa, babban jami’in shirin Sure-P, Abdul’aziz Shinkafi da kuma Bello Bindawa.

Su ukun ana tuhumwar su da salwantar da naira biliyan 5.7 na kudaden Sure-P.

An tuhume su da salwantar da kudaden da Sure-P ta tura jihar Katsina, bayan da hukumar ICPC ta yi bincike ta gano cewa sun saba ka’idar dokar kasa ta 2000.

Amma a ranar 27 Ga Nuwamba, Mai Shari’a Maikaita Bako ya kori karar bisa dalilin cewa mai gabatar da kara na gwamnatin tarayya ya kasa bayar da kwararan shaidun da ke nuna cewa an aikta laifin.

Dama kuma Ministan Shari’a kuma Antoni Janar Malami ne ya mika batun tuhumar a hannun gwamnatin jihar Katsina.

ASARKALAR SHARI’A A KATSINA

Cikin Oktoba, 2017, ICPC a madadin gwamnatin tarayyya, ta gabatar da kotu caji 17 a madadin gwamnatin tarayya, da ke yi wa jami’an gwamnatin su uku, kuma aka gurfanar da su a Babbar Kotun Jihar Katsina ta 3.

Amma kuma a ranar 25 Ga 2017, Antoni Janar na Katsina, Ahmed El-Marzuq, ya shaida wa gwamnati cewa jihar Katsina ta karbi shari’ar daga hannun ICPC.

El-Marzuq ya ce Malami ya rubuto masa takarda cewa ya karbi gabatar da shari’a a Katsina.

Daga inda sandar ta fara karkacewa, ko kuma aka tankwara ta, shi ne yadda Malami bai shaida wa ICPC damka shari’ar wadanda ake tuhuma su uku di na hannun gwamnatin jihar Katsina ba.

Dalili kenan a ranar 25 Ga October, 2017, lauyan ICPC, Nosa Omohigbo ya tubure a cikin kotu ya na kururuwar kin amincewa da jihar Katsina ta karbi shari’ar, domin ai ita ce ta kai kara.

Don me kuma za a damka wanda ake tuhuma a hannun wanda ya yi kara a ce ya yi masa hukunci?

Lauyana ICPC ya shaida wa kotu cewa hukumar fa ta rigaya ta kammala binciken ta, kuma ta samu hujjojin da ta dogara da su. Don haka dauke shari’a daga hannun gwamnatin tarayya a maida a hannun gwamnatin jihar Katsina, tamkar maida hannun agogo baya ne, kuma karya lakadarin yaki da cin hanci da rashawa ne.

BANGA-BANGAR MALAMI

Ita dai gwamnatin jihar Katsina ta karbi ci gaba da shari’ar jami’an uku daga hannun Antoni Janar kuma Ministan Shari’a na Najeriya, inda kuma Katsina ta kara kafa hujja da cewa an aikata laifin da ake zargin an aikata a cikin jihar.

An ce Malami ya bai wa Katsina damar karbar shari’ar a ranar 7 Ga Yuli, 2017.

Amma kuma ‘yan gaje-gani sun hakkake cewa an kintaci rana da watan da ya shude ne tun tuni aka rubuta, ba a lokacin ne ya bayar da umarnin ba.
A cikin takardar, Malami ya kafa wasu hujjoji da ya dogara da su har ya mika shari’ar a hannun gwamnatin jihar Katsina.

Sai dai kuma wani fitaccen lauya mazaunin Lagos, Jiti Ogunye, ya ce damka shari’ar wadda ICPC ce ta gabatar da ita a madadin gwamnatin tarayya, amma Malami ya maida ta a hannun Katsina, to tamkar farke wandon tsarin gurfanar da shari’a ce a tsakiyar kasuwa da nufin a ga tsiraicin tsarin.

Shi ma lauyan ya kawo karfafan dalilai da hujjojin sa na bayyana wannan ra’ayi da ya tsamo a cikin dokar kasa, wato kundin tsarin mulkin Najeriya.

SABATTA-JUYATTAR SIYASA YAYIN SHARI’AR JAMI’AN

Bisa shawarwarin da Malami ya bai wa jihar Katsina, sai aka zartas da hukuncin wanke jami’an daga dukkan laifukan da ake tuhumar su.

Sai dai kuma ba a yi hakan ba sai bayan sauya shekar da suka yi daga PDP zuwa APC.

Dama kuma su na cikin PDP ne suka yi laifin da ka zarge su da aikatawa.
Kafin sannan dai an kwashe sama da shekara daya ana kiki-kaka a kotu, domin neman wanda ya cancanta ya yi shari’ar tsakanin gwamnatin Tarayya ko kuma Gwamnatin Jihar Katsina.

Mai Shari’a Bako ya daukaka kara zuwa ranar 27 Ga Nuwamba, domin ci gaba da shari’a. sai dai kuma lokaci da ranar ta zo, katsahan sai lauyan gwamnati mai suna Aminu Ibrahim ya shaida wa kutu cewa gwamnatin jiha ba za ta iya ci gaba da shari’a ba, saboda ta kasa lalubo takardun bayanan shari’ar.

Daga nan sai lauyan ya nemi a daga kara har sai yadda hali ya yi.

Cikin haushin yadda ake ta karankatakaliyar wannan shari’a daga bangawren gwamnati, sai mai shari’a ta soke shari’ar kwata-kwata.

’Yan jaridar da ke cikin kotu a lokacin sun ruwaito cewa wadanda ake zargin su biyu sun rika dariya da murna da fara’a, har suna gode wa mai gabatar da kara bisa rawar da suke kallon ya taka wajen wanke su da Mai Shari’a ta yi.

BAYAN TIYA AKWAI WATA CACA

A wani jikon kuma kwatsam sai a ranar 28 Ga Agusta, 2018, El-Marzuq ya rubuta wa Malami wasika cewa a daina tuhumar jami’an na Katsina su uku da laifi.

Maimakon haka, a tsoma su cikin masu gabatar da shaida a kan wata shari’a da ake tukumar tsohon gwamnan jihar Katsina, Shehu Shema, a matsayin ganau daga masu bayar da shaidar Shema ya aikata laifukan da ake tuhumar sa. Kuma hakan aka yi.

Daya daga cikin hadiman Shema, Olubusola Olawale, ya bayyana wasikar da Malami ya rubuta cewa abu ne lullube mai wata boyayyar manufa.

Ya bai wa ICPC shawara ta nemi a sake shari’ar gaba daya bayan an maida mata gurfanar da wadanda ake zargin a hannun ta.

Share.

game da Author