Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Ike Ekweremadu da Shugaban Masu Rinjaye, Ahmad Lawan, sun rukume zazzafar gardamar bangaren da ya fi yawa tsakanin Sanatocin APC da na PDP a Majalisar Dattawa.
A yau ne Lawan ya bada wani kudiri, inda ya yi kira da jan hankali ga sauran sanatoci dangane da wani rahoto a kakafen yada labarai, wanda Lawan din ya ce kuskure ne.
Lawan ya ce an ruwaito cewa sanatocin PDP sun fi na APC yawa, abin da ya ce ba gaskiya ba ne.
Ya ce, Daily Trust ta ruwaito a shafin ta na 57 cewa, sanatocin APC su 57 ne, yayin da nan a PDP kuma su 58 ne.
Daga nan sai Lawan ya ce abin da ya sani, APC na da 56, ita kuma PDP na da 46.
Lawan ya kuma nuna wani kuskure da ya ce jaridar ta buga a shafi na 7, wanda ya ce ta buga cewa wadanda ba su yarda a amince da nadin Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa Festus Kiyamo ba, sun fi wadanda suka amince yawa, amma Shugaban Majalisa ya ce wadanda suka amince ne suka fi yawa.
Da ya ke maida masa raddi, Ekweremadu, wanda shi ke shugabancin majalisar a yau Alhamis, ya ce adadin da Lawan ya ce APC na su, zuki-ta-malle ce, ba gaskiya ba ne.
Ya ce babu wani kayyadadden lissafi ko tartibin adadin yawan na APC balle ma a ce sun fi na PDP yawa.
Batun amicewa ko zabe a majalisa kuwa, Ekweremadu y ace shugaba na la’akari ne da karfin muryoyin da suka fi sauti, ko masu cewa na msu cewa “e” ko kuma na masu cewa “a’a”.