El-Rufai ya yi Ta’aziyyar marigayi Sanata Aruwa

0

A sakon Ta’aziyya da gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya aikawa wa iyalan marigayi Sanata Ahmed Aruwa, El-Rufai ya ce Jihar Kaduna ta yi rashin mutum haziki sannan mashahurin dan kasuwa.

” Yau na tashi cikin bakin ciki tun bayan sanar dani rasuwar Sanata Aruwa da aka yi. Aruwa mutum ne mai kwazon gaske. Shahararren dan kasuwa ne, fitaccen dan siyasa sannan masoyin wasanni. Ya bada gudunmuwar sa matuka a wadannan fannoni.

” Allah muke roko da ya sa Aljanna ta zamo makomar sa. ”

Sanata Ahmed Aruwa ya rasu da safiyar Lahadi a wani asibiti da ke garin Kaduna. Sannan idan ba a manta ba ya wakilci Kaduna ta Tsakiya a majalisar Dattawa daga 1999 zuwa 2007.

Share.

game da Author