EFCC: Ku daina garkame gidajen wadanda ake zargi – Korafin Lauya Falana

0

Babban Lauya Femi Falana, ya shawarci Hukumar EFCC da ta daina garkame gidaje da kadarorin wadanda ake zargi da harkallar kudade.

Falana ya bayar da wannan shawara jiya Lahadi a Ikeja, Lagos, yayin gabatar da ‘Kundin Manyan Shari’un Harkallar Kudade a Najeriya.’

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), ya ruwaito cewa wannan kundi wanda ke kunshe da manya-manyan shari’u da bayanan harkallar kudade tare da makomar da abin ka iya haifarwa kan tattalin arziki, wata kungiyar kara Jama’a da Muhalli ce mai suna HEDA ta hardada bayanan aka tashi kundi daya dindi.

Yace haka kawai a kulle ko a garkame wasu kadarori na wanda ake zargi, alhali shari’a na kotu, ba a ma kai ga yanke masa hukunci ba, ba abu ne da ke da wani tasiri a ci gaban al’umma ba ne, domin an bar wannan kadara a cikin yanayi na ci gaba da karyewar darajar ta.

Sai yace har ma ya fi kyau idan ita EFCC din ta garkame kadara ko ginin kantuna ko gidaje, to a yi amfani da su kafin a kai ga yanke hukunci.

“Idan wani ya saci kudi ya gina asibiti, kamar wanda ke kan titin Adeniyi Jones da ke Ikeja, misali a ce wani ya saci kudi ya gina asibitin a kan kudi naira bilyan 2.5, to yanzu ga shi can an garkame shi.

“To ni dai ina ganin cewa hukumar da ta yi haka, ba ta shuka wa al’umma abin alheri ba, har cda ta kulle asibiti, ta makala masa: “Bincike ake yi”.

“Haka abin ya ke a sauran gidaje. Ga jama’a na neman gidajen haya. Kai kuma ka je ka kama gidajen mutane ka garkame, alhali kotu ba ta tabbatar da laifi a kan wanda ake zargi ba fa.

“Kuma wasu shari’un sai sun kwashe shekaru masu yawa ba a kai ga yanke hukunci ba. To ya zuwa lokacin da za sake bude gidajen, darajar su ta zube, wani sashe ya lalace, jama’a ba za su yi sha’awar shiga ko saye ba.”Inji Falana.

Ya ce shi dai a sanin sa, an kafa EFCC ce domin ta farfado da kasuwanci da tattalin arziki, ba wai su karya tattalin arziki ba.

Ya kuma nemi dalilin da ya sa za a kame motoci a zube su shekaru da yawa a tsaye, ba tare da ana amfanar su ba.
Sai ya bayar da shawarar cewa kamata ya yi EFCC ta sayar da motocin, ta ajiye kudaden a banki, har zuwa lokacin da aka kammala shari’a.

“Idan kotu ta bai wa gwamnati rashin gaskiya, sai EFCC ta bai wa mai motocin kudaden sa. Idan kuma shi aka bai wa rashin gaskiya, to kudaden sai gwamnati ta rike, tunda kotu ta tabbatar da cewa na gwamnatin ne.”Cewar Falana.

Share.

game da Author