Babban Hafsan Hafsoshin Askarawan Najeriya, Tukur Buratai, ya gargadi sojojin da ke yaki da Boko Haram a Yankin Arewa maso Gabas da su yi kaffa-kaffa da farfagandar da ake yadawa a kan yaki da ta’addanci.
A cikin sakon murnar zagayowar Kirsimeti da ya aika wa sojojin a jiya Talata, Buratai ya kara nanatawa cewa kokarin da sojojin suka yi ya nuna cewa lallai an samu galaba kan Boko Haram.
“Dalili kenan a yanzu suke yada farfagandar karairayi domin su sare muku guiwa suna bayyana irin karfin da suke yi wa jama’a cewa wai su na da shi.
“Amma ya na da kyau sojoji su gane cewa ai Boko Haram ba fa wata tsiya ba ce, kawai dai wasu gungun mabartana ne.
“Don haka tilas ku tashi tsaye ku bankado sauran burbishin su da suka rage.
“Mun fa fi su samun horo da gogewar iya fafata yaki, mun fi su kayan fama kuma mun fi su kwarewa. Kuma mu na da tarihin samun nasarori a fagagen fama a nan gida Najeriya da kuma kasashen waje.”
Buratai ya kuma jinjina musu da gode musu a kan namijin kokarin da su ka yi wajen jajircewa da sadaukar da rayukan su a cikin 2018.
Daga nan sai ya hore su da su kara zage damtse domin a-yi-ta-kare a cikin 2019.