Kwanaki kadan bayan da dillalan man fetur suka yi wa gwamnatin tarayya barazanar jefa kasar nan cikin matsanancin wahalar fetur, idan ba ta biya su kudaden bashin tallafin mai n a naira bilyan 800 da suke bin gwamnatin ba, an yi masu tayin fara biyan su naira bilyan 340.
Su na bin gwamnatin tarayya bashin wadannan makudan kudaden ne a karkashin yarjejeniyar PSF da gwamnati ta tsara.
Sai dai kuma dillalan sun ki amincewa da wannan tayin musamman ganin cewa ba madarar kudin ba ne za a zube musu a banki ba, takardar alkawarin karbar kudin ne aka ce za a ba su, wadda a Turance ake kira ‘Promisory Note’.
Ministar Harkokin Kudade, Zainab Ahmed ce ta shaida wa PREMIUM TIMES haka, cewa za a ba su kudaden a kan rubutaccen alkawari na ‘promisory note’ da za a ba su nan da makonni kadan.
Su kan su wadannan kudaden alkawarin, ba za su samu a rubuce ba tukunna har sai an kai batun a gaban Majalisar Tarayya an amince tukunna.
Tuni dai dillalan man fetur din suka yi fatali da wannan tayi da gwamnatin tarayya ta yi musu.
Sun sake yin barazana irin wadda suka yi a cikin wancan makon cewa za su sallami ma’aikatan su ta yadda aikin lodi, saukale da jigilar mai ba za ta yiwu a dukkan rumbuna da daffo-daffon manyan ajiyar fetur na kasar nan da suka mallaka wadanda kamfanin NNPC ke amfani da su idan kamfanin ya shigo da man fetur daga waje ba.
Manyan dillalan man fetur din sun ce rubutacciyar takardar alkawarin da gwamnati ta ce za ta ba su, ba za ta yi musu amfani ba wajen biyan ma’aikatan su albashi da kudaden alawus-alawus ba.
Sun kuma yi korafin cewa bankuna sun rike musu kadarori saboda sun kasa biyan bankunan kudaden da suke bin su.
Dillalan sun ce sun afka cikin wannan kiki-kaka ne, saboda gwamnatin tarayya ta rike musu kudi har naira bilyan 800. Sun ce hakan ne ya sa suka kasa biyan basuka ga bankuna, kuma suka kasa biyan dimbin ma’aikatansu albashi da alawus-alawus.
Sun ce babu ruwan su da wata takardar alkawari, ‘alert’ kadai su ke so su ji ya shiga cikin asusun ajiyar bankunan su.