Shugaban riko na Hukumar EFCC, Ibrahim Magu, ya bayyana cewa hukumar sa ba ta ma bukatar a ba ta har tsawon sa’o’i 72 ta gurfanar da tsohuwar ministar man fetur, Diezani Allison-Madueke a gaban kotu.
Ya ce matsalar da kawai EFCC ke fuskanta, ita ce ba a cikin Najeriya matar ta ke zaune ba.
Magu ya furta wannan bayani ne jiya Laraba a lokacin da ya ke tattaunawa da manema labarai a ofishin sa, cikin harabar hedikwatar EFCC, da ke Jabi, Abuja.
Daga nan ya ci gaba da cewa EFCC za ta ci gaba da bin umarnin da kotu ta bayar na a gurfanar da Diezani. Ya ce idan har EFCC ba za ta iya ba, to za ta daukaka kara ce a kan wannan umarni da Babban Kotun Tarayya ta yanke.
“Amma inda matsalar ta ke, Diezani ta na a wata kasa zaune, kuma a can din ma ta na fuskantar tuhuma. Wannan shi ne halin kaka-ni-ka-yin da muka tsinci kan mu a ciki.”
Ya ci gaba da cewa amma su na nan su na ta kokarin ganin cewa an dawo da ita, “tunda dama matakin farko shi ne a shigar da kara kotu, kuma an shigar. Sai mataki na biyu, kotu ce za ta bada iznin a kamo ta, kuma ta bayar din. Sai dai kawai ta na wata kasa ce a yanzu ta ke zaune. A can din ma, tuhuma ta ke fuskanta.” Inji Magu
Da ya ke magana a kan kudaden da aka sace ake kokarin dawo da su daga kasashen ketare, ya ce har yanzu akwai kashi 80 bisa 100 na kudaden da aka sace, su na kasashen duniya jibge.
“A Ingila akwai dala milyan 300 a jigbe, wadanda sai yi gumin goshi, an yarfe kafin a iya dawo da su.
Discussion about this post