A ranar Laraba ne shugaban jami’an tsaro ‘Civil Defence Corps (NSCDC)’ dake aiki a yankin arewa maso gabashin kasar nan Abdullahi Ibrahim ya bayyana cewa sun kama wasu mata biyu ‘yan kunar bakin wake a tashar motoci dake Barno.
Ibrahim ya ce bincike ya nuna cewa daya daga cikin matan mai suna Fatima Kabir matar Mamman Nur ne daya daga cikin shugabannin kungiyar Boko Haram.
” Mun kama Fatima Kabir da Amina Salihu a wannan tashar motoci dake Barno a makon da ya gabata yayin da suke kokarin shiga mota zuwa Maduguri domin kai hari.
Ibrahim ya kuma bayyana cewa rundunar su ta yi nasarar kama ‘yan Boko Haram 40 sannan dukkan su sun tuba yanzu.
A karshe yace a yanzu haka jami’an Civil Defence 1000 ne ke aiki a jihohin Arewa Maso Gabashin Kasar nan.
Discussion about this post