Cocin RCCG zai ciyar da mutane milyan 50 a cikin watan Disamba

0

Cocin da aka fi sani da suna RCCG, wato Redeemed Christian Church of God, ya kafa wata gidanuniyar ciyar da marasa galihu har a cikin watan Disamba din nan.

Gidauniyar za ta kuma maida hankali wajen magance wa wasu milyoyi matsalolin kasa daukar nauyin ilmi, kula da lafiya, matsananciyar yunwa, tallafin kananan sana’o’i da kuma farfadowa ko gyaran halaye da babi’un kangararru.

Daya daga cikin manyan jami’an shirin, Idowu Iluyomade ne ya bayyana wa manema labarai haka a wani taron da ya kira su a Lagos.

Idowu ya ce gidauniyar ta cocin RCCG ya na da cibiyoyi 42, 796 a Najeriya kadai, kuma ya na wasu da dama a cikin kasashe 197 na duniya.

Pastor Enoch Adebayo ne shugaban wannan coci.

Share.

game da Author