Kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta bayyana cewa mutane 100,000 a duniya ne kan rasa rayukan su a dalilin cizon macizai duk shekara.
WHO ta kuma bayyana cewa a Najeriya mutane 10,000 ne macizai ke cizo duk shekara sannan har yanzu babu tabbacin adadin yawan dake mutuwa a sanadiyyar haka.
Ma’aikatan kiwon lafiya ta yi kira ga mutane da su ci gaba da kula da kan su da yin hatara musamman a wannan lokaci na hunturu.
Sun ce dafin maciji na iya sanya makanta,shanyewar bangaren jiki, yanke bangaren da maciji ya sara ko kuma mutuwa idan ba a gaggauta daukar mataki ba.
Idan ba a manta ba a kwanakin baya PREMIUM TIMES ta ruwaito cewa mutanen jihohin Gombe da Filato basu da sukuni a dalilin yawa-yawan cizon maciji da ya addabe su.
Bisa ga rahotan mazauna karkara da manoma ne suka fi fama da wannan matsalar sannan rahotan ya kara nuna cewa kashi 8.7 ne kawai daga cikin su ke zuwa asibiti domin samun magani.
” A Mafi yawan lokutta idan maciji ya ciji mutum sai a nemi maganin gargajiya inda a dalilin haka mutane ke mutuwa saboda rashin ingancin da magungunan gargajiyar ke da su.
Ma’aikatan kiwon lafiyar ta bayyana wasu hanyoyin da za su taimaka wajen hana macizai zama a muhalli da cikin gidaje
1. A daina barin tagogi da kofofi a bude ba tare da a na kula da duk wani motsi ba. Za a iya saka murfin kofa mai raga, kafin ainihin kofar shiga saboda kiyaye wa.
2. A tabbata an duba rassan itatuwa da kuma tarin ganye dake karkashin itatuwan da suke domin macizai za su iya zama a irin wadannan wurare.
3. Tattabata an tsaftace muhalli kamar su nome ciyawa da kawar da karikitan kaya domin hana samar da wurin kwanciya ga macizai.
4. Za a iya yin amfani da tafarnuwa domin hana macizai shiga cikin gida da zama a muhalli.
5. A tabbatar an kakkabe wurin kwanciya kafin a kwanta domin wasu macizan na iya boyewa a wurin kwaciyar mutum.
Abin da ya kamata a yi idan maciji ya sari mutum.
1. A gaggauta ba wanda maciji ya sara maganin kawar da ciwon jiki.
2. Kada a huda wurin da maciji yayi sara domin hakan na iya kawo zuban jini.
3. Kada a yawaita motsa wajen da maciji ya yi sara domin hakan na iya sa gubar macijin shiga wasu bangarorin jikin mutum.
4. A kwantar da wanda maciji ya sara ta gefe koda zai yi amai.
5. Kada a yi amfani ko kuma a sha maganin gargajiyya amma a gaggauta zuwa asibiti domin samun kulan da ya kamata.