Shugaba Muhammadu Buhari ya kafa kwamitin da zai tantance cin gashin kan Majalisar Jihohi da Fannin Shari’u na Jihohi, daidai da yadda zai tafi kafada-da-kafada da gyara na hudu na dokar kasa ta 1999.
Kakakain Yada Labarai na Buhari, Femi Adesina ne ya bayyana haka inda ya kara da cewa Kwamitin Shugaban Kasa zai yi aiki ne a bisa tabbatar da cewa har sai ya kai ga samar da damar cin gashin kai ga majalisar dokoki ta jiha da kuma bangaren shari’a na kowace jiha.
Ministan Shari’a kuma Antoni Janar na Tarayya, Abubakar Malami shi ne zai kasance shugaban kwamitin, yayin da Ita Enang, zai kasance Sakataren kwamiti.
Kwamitin na da wakilai daga bangaren shari’a da suka hada da Babban Jojin Jihar Kogi, N. Ajanah da kuma K. Abiri na jihar Bayaelsa.
Sauran sun hada da Babban Khadi na jihar Gombe, Abdullahi Maikano Usman da ke Kotun Daukaka Kara ta Shari’ar Musulunci ta jihar Gombe da kuma Mai Shari’a Abbazih Musa Sadeeq, Shugaban Riko na Kotun Daukaka Kara na Gargajiya, na Yankin Babban Birnin Tarayya, Abuja.
Majalisaun Jihohi za su samu wakilcin Mudashiru Obasa, wanda shi ne Shugaban Kungiyar Kakakin Majalisa na Najeriya, wanda kuma shi ne Kakakin Majalisar Jihar Lagos da kuma Abel Riah, Kakakin Majalisar Jihar Taraba. Akwai sauran mambobin da za su wakilci bangarori da dama a cikin kwamitin.
Discussion about this post