Shugaba Muhammadu Buhari ya gargadi wadanda ya nada kan mukamai, shugabannin jam’iyya da jami’an gwamnati cewa su guji yin amfani da mukaman su wajen afkawa hanyoyin harkalla, kulle-kulle da rarume-rarumen kudade.
Babban Mai Taimaka Wa Shugaban Kasa a Fannin Yada Labarai, Garba Shehu ne ya bayyana haka a cikin wata takarda da ya aiko wa PREMIUM TIMES.
Shehu ya ce masu amfani da sunan Shugaban Kasa ko amfani da mukaman su sun a karbar kudade da sunan yi wa jama’a wata alfarma a cikin gwamnati, su na tozarta gwmnatin Shugaba Buhari.
Shehu ya ce Buhari ya jaddada da babbar murya tun farkon hawan sa a kan mulki cewa ba zai lamunci jami’an gwamnatin sa ko mukarraban sa su rika amfani da mukaman su domin tara dukiya ba.
Ya kuma ce Buhari ya kara jaddada aniyar sa ta kakkabe cin hanci da rashawa ta hanyar kakkabe wadanda duk ba su bi sahun tafiyar tsarin mulkin sa na yaki da rashawa ba, sannan kuma a hukunta su.
Daga nan ya ce Buhari ya yi kira da a kai rahoton duk wani jami’in gwamnati ko mukarraban sa da ya nemi alfarmar a biya shi wasu kudi kafin ya yi wani aikin da ke bisa ka’ida.
Buhari ya yi wannan gargadi ne kwanaki kadan bayan jami’an SSS sun kama wata mata mai suna Amina Mohammed da laifin yin amfani da sunan uwargidan Shugaban Kasa, Aisha Buhari ta na karbar makudan milyoyin kudade a hannun wadanda tsautsayin damfara ya fada kan su.