Buhari bai dauki neman tazarcen sa ‘ko a ci ko a mutu ba’

0

Ministan Harkokin Kasasshen Waje, Geoffrey Onyeama, ya ce Shugaba Muhammadu Buhari bai dauki kamfen na yakin neman sake zaben sa karo na biyu, ko a ci ko a mutu ba.

Onyeama ya ce Buahri zai yi matukar marhabin da sakamakon da jama’a suka zabar wa kan su a zaben 2019.

A cikin wata tattaunawa da Onyeama ya yi da Kmfanin Dillancin Labarai, NAN, ya ce shi fa Buhari abin da kawai ke gaban sa shi ne ya samar da yanayin da kowace jam’iyyar sisaya za ta shigo a yi goyayya da ita.

“Buhari ya maida hankali sosai wajen ganin cewa zaben 2019 ya tabbata mai inganci, sahihi kuma karbabbe ga daukacin jama’a.

Ya ce abin da jama’a suka zaba, shi sakamako zai bayyana.

“Buhari ba ya yi wa INEC katsalandan, kuma ya na so INEC ta zama cikakkar mai cin gashin kan ta, ta yadda za su yi abin da ya dace kowa ya yaba wa hukumar.

Share.

game da Author