Boko Haram sun sake kashe da dama a sabon harin da suka kai wa sojoji a Gudumbali

0

Harin da Boko Haram suka kai wa sojoji a Gumbali daidai almurun Juma’ar da ta gabata, ya haifar da asarar rayuka da dama, kamar yadda majiyar jami’an sojoji a jihar suka bayyana.

Sai dai kuma sojojin sun ce soja daya ne kadai ya rasa ran sa a harin da aka kai musu.

Haka dai kakakin yada labarai na Operarion Lafiya Dole ya bayyana.

Sun kuma ce sun samu galabar korar maharan tare da kashe da dama daga cikin su.

Gudumbali can ne hedikwatar Karamar Hukumar Guzamali, inda aka kashe sojojin Najeriya da dama a sansanin su da ke Metele, kan iyaka da kasar Chadi.

Wata majiya daga cikin manyan jami’an, ta shaida wa PREMIUM TIMES daga garin Damasak cewa Boko Haram sun yi wa sojojin kwanton-bauna ne, wato suka same su ba a cikin shiri ba, a daidai lokacin da za a fara raba musu abincin dare.

“Boko Haram sun ritsa sojojin ba a cikin shiri ba, saboda a lokacin duk sun fito ne, sun yi dafifi motar da ke kai musu abinci na tsaye suna kokarin karba.’

Haka wata majiya ta shaida wa PREMIUM TIMES, amma ta ce a boye sunan ta.

“A lokacin mafi yawan su ba a cikin kayan fama su ke ba, ballantana kuma a yi maganar dauke da makamai, a lokacin da Boko Haram suka bude musu wuta daga kowace kusurwa.”

Majiyar PREMIUM TIMES da ke Damasak, garin da ke kusa da iyakar Najeriya da Nijar, mai nisan kiomita 76 daga Gudumali, ya bayyana mana cewa mahara sun tarwatsa sansanin na Gudumali.

“Akwai sojoji kusan 700 a sansanin Gudumali, amma da yawan su tserewa a guje suka yi, su kuma wadanda aka bude wa wuta, kwanan su ya kare.

Ya kara da cewa a jiya Asabar an yi kokarin kwaso gawarwakin sojojin da aka kashe din.

“Maganar da muke yi muku a yanzu ga mu nan a Damasak, tare da gawarwaki 30 na sojojin mu da aka kashe. Sannan kuma wadanda suka samu tserewa kamar su 20, a kafa su ka iso har nan Damasak. Har yanzu ba mu tatance sauran yawan sojojin da aka kashe ko suka tsere suka kubuta ba.”

Share.

game da Author