Rahotannin da ke fitowa daga majiya mai tushe, sun tabbatar da cewa ‘yan ta’adda sun kama garin Baga, bayan wanin kazamin fada da suka yi da sojojin Najeriya.
Dama tun a jiya PREMIUM TIMES sai da ta buga labarin yadda Boko Haram suka kai wa sojoji hari a sansanin Baga da ke bakin ruwa a ranar Laraba.
Sojojin Najeriya sun tabbatar da kai harin, amma sun ce an kori ‘yan ta’addar.
Amma kuma wani rahoto da ke fitowa daga majiyar sojoji na nuna cewa Boko Haram din ba su gudu daga garin mai arzikin kasuwanci ba, har a jiya Alhamis cikin dare sun a cikin garin.
Majiya ta ce su ne ke rike da garin kuma hatta karin taimakon sojoji da CJTF da aka kai, sai da Boko Haram suka yi musu kwamton-bauna. Tilas suka juya suka koma inda suka fito.
Majiyar ta ce an kai musu harin kwanton baunar ne a Kauwa, wani kauye da ke kilomita 30 tsakanin sa da Baga.
“A yanzu haka Birged Kwamanda da manyan sojoji 3 da kuma kananan sojoji 21 sun iso nan Monguno da karfe 4 na yamma.”
Majiyar ta kara da cewa a na sa ran isar wasu karin sojojin da suka tsira daga harin yayin da wadanda suka ji ciwo kuma fararen hula sun dauke su zuwa Maiduguri.
“An kuma bayyana cewa Boko Haram sun yi wa jama’ar da suka rage a garin Baga jawabin gargadin cewa wanda ya yi amsu zagon-kasa zai dandana kudar sa.
Sashen Hausa na Radiyon BBC ya ruwaito a jiya Alhamis cewa Boko Haram ne ma suka yi Limancin sallar Asubahi ta asubar jiya Alhamis.
Majiya ta shaida wa BBC Hausa cewa, ya tafi sallar Asubahi, sai kawai ya ga mutane dauke da manyan bindigogi a masallacin.
Ya ce sun shaida masa cewa babu ruwan su da farar hula, ba za su kashe kowa ba.
Sun kuma shaida masu cewa su ‘yan kungiyar IS ne masu mubaya’a ga bangaren Boko Haram a karkashin jagorancin Mamman Nur.
Dama garin Baga wanda cibiya ce ta hada-hadar cinikin kifi, ya taba fadawa a hannun Boko Haram cikin 2015, amma daga baya sojojin suka kwato shi tare da taimakon sojojin Nijar da na Chadi.
Matsalar isa inda garin yarin ya ke da kuma yawan hare-hare daga Boko Haram ke sa ana kasa tantance hakikanin abin da ke faruwa a garin.