Boko Haram ba su kwace garin Baga ba – Rundunar Soji

0

Babban kwamanda na sashen koyar da sojojin Najeriya dabarun yaki Lamidi Adeosun ya bayyana cewa Boko Haram basu kwace garin Baga ba kamar yadda aka yi ta yadawa a kafafen yada labarai.

Lamidi ya ce tabbas dakarun Najeriya sun yi arangama mai zafi da mayakan Boko Haram a garin Baga, sai da Sojojin ne suka yi nasara a kan ‘yan Boko Haram din.

Idan ba a manta ba PREMIUM TIMES ta ruwaito daga sahihin majiya cewa a wannan bata kashi da aka yi tsakanin Boko Haram da Sojojin Najeriya, Boko Haram ne suka sami galaba a wannan arangama inda har suka kwace garin Baga.

Bayan haka ne Lamidi a taron manema labarai da aka yi a garin Maiduguri ya bayyana musu cewa a yanzu kam sojojin Najeriya ne suke da iko sannan suke rike da garin Baga din.

Share.

game da Author