Hukumar Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), ta bayyana cewa a jihar Barno ta kara yi wa ‘yan gudun hijira har 2046 a cikin kwana daya a fadin jihar.
Rajistar da aka yi musu a ranar Talata, NEMA ta ce masu gudun hijirar sun fito ne daga garuruwan Kukawa, Kauwa, Doron Baga Kekeno da kuma Bunduram da ke Karamar Hukumar Baga ta Jihae Barno.
Wadanda aka yi wa rajistar, dukkan su sun fito ne daga gidaje 204 daga wadannan kauyuka da aka lissafa a sama, saboda tsananin hare-haren Boko Haram da suke fuskanta.
An tattara wadannan masu gudun hijira ne a karkashin NEMA ta jihar Barno da kuma Kungiyar Kasa-da-kasa Mai Lura Masu Gudun Hijira ta Duniya, a sansanin ‘Teachers’ Village’ da ke Maiduguri.
Shugaban NEMA na jihar Barno, Mohammed Garga ne ya bayyana haka.
Discussion about this post