Bayan kwanaki 105, matasa masu kirgen buhun gero sun ce bai kai yawan ‘yan Najeriya ba

0

Idan ba a manta ba wasu matasa a jihar Kebbi sun dage sai sun kirge buhun gero tas domin sanin ko kwayan gero nawa ne ke cikin wannan buhu.

Wannan himma na matasan nan ya samo asaline tun bayan musu da suka yi a wajen hirar su wato majalisar su cewa buhun gero yafi yawan ‘yan Najeriya.

Daga nan ne fa suka kwance buhun gero suka ko fara kirgawa ganin cewa wasu daga cikin su sun karyata wannan magana.

Matasan sun dauki sama da watanni uku da rabi suna kirga wannan gero.

Bayan sun kammala, sai suka sanar da sakamakon kirgen su inda kakakin wannan matasa Ahmed Sarkin Yaki ya bayyana wa taron mutane a wajen bukin sanar da sakamakon kirgen a fadar sarkin Yauri, inda ya bayyana cewa buhun gero bai kai yawan mutanen Najeriya ba.

” Ina so in sanar muku cewa bayan kwanaki 105 da muka yi muna kirga buhun gero, sakamakon kirgen ya nuna cewa akwai kwayan gero 11,979,868 ( Miliyan Goma Sha Daya da Dubu Dari Tara da Sabain da Tara da Dari Takwas da Sirtin da Takwas). Hakan ya nuna cewa buhun gero bai kai yawan ‘Yan Najeriya ba.”

Mutane da dama sun halarci taron bayyana sakamakon kirgen.

Sai dai kuma a yayin da matasan suka yi haka don warware wani musu da suke yi wasu na ganin rashin aikin yi ne kawai ya sa suka yi haka.

Gwamnan jihar Kebbi ya jinjina wa matasan bisa wannan kokari da suka yi sannan ya bayyana cewa ba rashin aiki bane ya sa suka yi haka domin kuwa ba mutane bane masu zaman kashe wando.

Share.

game da Author