Kwanaki kadan kafin ya cika shekaru 77 a duniya. Jaridar THE CREST ta samu zantawa da shi a gidan sa da ke Minna, inda ya yi bayani kan batutuwa da dama, kamar yadda za ku karanta, bayan PREMIUM TIMES ta samu amincewar The Crest ta fassara tattaunawar.
Karanta nan: Ban taba fargaba ko tsoron shirya juyin mulki ba – Babangida
TAMBAYA: Juyin mulkin da sojoji suka yi a ranar 29 Ga Yuli, 1966, ya sauya alkiblar akalar kasar nan da kuma tarihin ta gaba daya. Ina maganar juyin mulkin ramuwar-gayya, wanda kai ma ka shiga ciki. Wace rawa ka taka a cikin juyin mulkin, kuma me ya ja hankalin ka ka shiga cikin masu yin juyin mulkin?
IBB: Abu ne mai sauki ya ja hankali na. Ka ga su dai wadanda suka yi juyin mulkin farko, sun samu nasarar kiran juyin mulkin na bangaranci, inda suka kashe akasarin mutanen da muke girmamawa da kallon shugabannin mu. Sun kashe irin su Burgediya Samuel Ademulegun da matar sa, Burgediya Zakari Maimalari, Kanar Kur Mohammed da sauran su.
To mu da ke kananan hafsoshin soja a lokacin, wadanda aka kashe mana din nan su ne muke kallo abin koyi. Sannan idan aka koma bangaren shugabannin siyasa. Sun kashe Sir. Ahmadu Bello da Tafawa Balewa da Cif Samuel Ladoke Akintola.
Ta kasance duk inda ka zauna maganar juyin mulkin ake yi, a sarari babu wani boye-boye.
Hatta a gidajen radiyo da jaridu maganar da aka rika yi kenan, cewa wani bangare ne ya yi wa wasu bangare juyin mulki. Ba zan manta ba wata jarida ta kasar Ghana har ma ta buga hoton Sardauna kwance bayan an bindige shi.
Wannan hoto da aka buga ya harzuka jama’a da dama, ciki kuwa har da mu kananan hafsoshin sojoji.
Ashe ka ga lokacin da yin juyin mulkin ya kusanto, ba a ma dauki wani tsawon lokaci ana tsara shi ba. Dama abu ne na ramuwar-gayya.
TAMBAYA: Ana ganin wannan juyin mulki ya fi muni wajen zubar da jini a tarihin Najeriya da Afrika gaba daya.
IBB: E mana, saboda ya nemi ya wuce gona-da-iri.
TAMBAYA: Ta yaya?
IBB: An yi abin da aka ga damar yi. Manyan jami’an sojoji sun kyale abubuwa sun rincabe. Hatta masu a cikin sauran farabiti, ko masu mukamai sun dauki doka a hannun su. Abin ya yi muni, kuma abin takaici ne da hakan ta faru.
TAMBAYA: Ko ka na da-na-sanin shiga cikin wannan juyin mulki?
IBB: A’a. Ba na da-na-sani.
TAMBAYA: ’Yan Najeriya na yi maka kallon mutumin da ya kware wajen iya kitsa kutunguila, kulla tuggu da kuma shirya bagarad da mutane – yadda idan ka ce jama’a bi nan, kai kuma sai ka baude ka bulla ta can. Wato dai irin halin ka irin halin shahararren dan siyasar nan na Italy da aka yi, mai suna Machiavelli.
IBB: A’a, ba haka ba ne. A daina hada ni da Machiavelli. Tsakani na da Machiavelli hanyar jirgi daban, ta mota ma daban. Ai na fa dade da karanta tarihin sa tun tuni.
TAMBAYA: Jama’a da dama sun yi imani da cewa ka samu damar da za ka kafa kyakkyawan tarihi har abada a kasar nan.
Sun ce ka fara gudanar da mulki lafiya kalau a kan hanya mai kyau, ka fito da shirye-shiryen mika mulllki ga farrrar hula, amma daga nan kuma sai ka rika daga rana yau, gobe ma ka daga rana, jibi ma haka. Har dai ta kai mu ga rudanin 12 Ga Yuni. Me za ka ce?
IBB: Wato ni ina ganin jama’a ba su yi min adalci ba. Domin tun farkon shirin komawa mulkin farar hular da muka fito da shi, ai na shiga kafafen watsa labarai, na yi bayanin cewa za mu fara abin nan mataki-mataki, domin ai koyo muke yi a lokacin.
Kowa ya san nace idan muka ci karo da wani cikas, to za mu rika dakatawa, sai mu canja salo ko taku, sannan mu cira gaba. Don haka ni dai a wannan batu, ban yi wa ‘yan Najeriya wani dungu ko kumbiya-kumbiya ba. Na fada musu komai tun daga farko. Amma a lokacin hankalin kowa ya karkata a kan cewa sojoji su sauka daga mulki kawai. Amma tun da farko sai da muka yi gargadin cewa idan aka samu cikas a kan hanyar tafiyar mu ta komawa ga mulkin dimokradiyya, to za a sauke kaya, a kimtsa lodi, a dora sannan a yi gaba. Wannan shi ne ya kai mu ga rudanin 12 Ga Yuni.
TAMBAYA: Ana ganin zaben 12 Ga Yuni ne ya fi kowane zabe inganci a tarihin zabukan kasar nan. Haka kai ma ka ke gani?
IBB: Kuma sai ba a jinjina min ba tunda zaben ya fi kowane inganci.
TAMBAYA: An jinjina maka mana, amma ana ganin kai ne da kan ka ka buge hannayen da aka yi maka jinjinar da su, aka koma ana hantarar ka. Wai ya aka yi haka ta faru ne?
IBB: To haka dai mutane ke ta cewa. Ko oga na Obasanjo abin da y ace min kenan. amma ai daga baya da ni da shi muka zauna na baje masa a faifai abinda ka iya zuwa ya dawo.
TAMBAYA: Mene ne zai iya faruwa idan aka fadi sakamakon zaben? Kai ne fa shugaba a lokacin, kuma duk abin da ka fada ta zauna, ya zama doka.
IBB: Kwarai haka ne, amma abin da zai iya faruwa bayan sanar da sakamakon zaben shi ne abin dubawa.
TAMBAYA: Shin mene ne zai iya faruwa?
IBB: Watakila za ka abin da zai iya faruwa idan da an bayyana sakamakon zaben a cikin littafin da kila zan rubuta.
TAMBAYA: Amma ai ka ki rubuta tarihin ka.
BABANGIDA: Inji wa? Ina rubutawa mana. Ana ma kan aikin.
TAMBAYA: Ashe littafin ya kusa fitowa kenan?
IBB: Ina karasa kammalawa ne, ya kusa fitowa, nan ba da dadewa ba.
TAMBAYA: An ce Abacha ya rika nuna maitar sa a fili ta son mulkin kasar nan. Shin wannan dalili ne ya sa ba a bayyana sakamakon zaben ba? Kuma da gaske ne Abacha ya yi maka barazanar cewa shi ma fa ya na so ya zama shugaban kasa, shi ya sa ka soke zaben 12 Ga Yuni?
IBB: A’a, ai bai yi min barazana ba. Zan iya yi masa wannan adalcin. Amma dai na san ya so ya yi mulkin kasar nan sosai da sosai. Ka jira, za ka karanta komai a cikin littafi na.
TAMBAYA: Shin wai barazana ce ka fuskanta ga rayuwar ka ko kuma kasar ce ta fuskanci wata barazana wadda ta hana ka amincewa a bayyana sakamakon zaben.
BABANGIDA: Ni babu wanda yay i wa rain a wata barazana. To ni kuwa wane dare ne jemage bai gani ba? A yanzu haka a cikin jiki na akwai harsashi, kuma ina rayuwa ta tare da shi.
Amma dai a zubin yadda mu ka tsaro makomar kasar nan, sai muka ci karo da abin da zai iya dagula mata al’amurra, to za mu iya hana abin faruwa. Don haka a nan, na dauki nauyi da alhakin soke zaben 12 Ga Yuni, a bisa wannan dalili da na bayar.
TAMBAYA: Shin shi wanda ya ci zaben ne idan ya zama shugaban kasa ba zai zame wa Najeriya alheri ba, sai ka soke zaben, aka ki fadar sakamako?
IBB: Ni dai ban ce haka ba. Mutumin nan fa ya yi yakin neman zabe, mutanen kasar nan suka ga shi ne zabin su, kuma aka zabe shi a zaben da babu hargitsi, mafi tsafta a zaben Najeriya.
TAMBAYA: Yanzu kai ka yarda Abiola ya ci zabe?
IBB: A’a, amma dai ya na kan hanyar lashe zabe aka dakatar da sanarwa. Saboda a lokacin ai sakamako daga yankuna da jihohi bai gama kammaluwa wuri daya ba. Ashe kenan tunda ba a kammala tara kuri’u an gama lissafi ba, har aka sanar da wanda ya yi nasara, to zan yaudari kaina idan na ce Abiola ya ci zaben 12 Ga Yuni.