Ba za su zabi dan takarar da bai goyi bayan dalibai mata saka hijabi ba’ – Kungiyar MSSN

0

Kungiyar Dalibai Musulmi ta Najeriya, Reshen Jihar Lagos, ta bayyana cewa a zaben 2019 mai zuwa ba za ta yi zabe ido-rufe ba.

Kungiyar ta MSSN ta ce a zaben gwamna da na sanatoci da mambobin jihar da tarayya, sai ta tsaya ta darje, ba za ta zabi duk wani dan takarar da bai goyi bayan dalibai mata su rika saka hijabi a makarantu ba.

A cikin wata sanarwa da Shugaban MSSN reshen jihar Legas, Saheed Ashafa ya fitar jiya Alhamis, ya ce kungiyar su ba ta siyasa ba ce, kuma babu ruwanta da batun siyasa.

Sai dai kuma ya ce amma a wannan zaben ba za su zauna su zabi duk wani dan siyasar da ba ya so ko ba ya kishin ganin dalibai mata musulmi sun saka hijabi a makaranta ba.

Ya ce wannan ce kawai hanyar da za su iya yin nasara a kan batun tunda su ba fitowa suke yi a yanayi na cikin rigima su na neman a biya musu hakkokin su da ake tauyewa ba.

Ashafa ya ce tuni dama kungiyar MSSN ta wayar da kan miliyoyin mambobin ta a lokuta da dama a fadin jihar cewa su mallaki katin zabe, kuma sun mallaka, domin kwatar ‘yancin su na saka hijabi a makarantu.

Ya ce a wannan karo za su yi amfani da katin jefa kuri’a domin su share hawayen da ke ta kwarara a fuskokin su sakamakon tozartawa da musguna wa dalibai mata musulmi da ake yi, ta hanyar kin amincewa a kafa dokar da za ta ba su ‘yancin saka hijabai a makaranta.

Ashafa ya kuma hori shugabannin makarantun sakandare su daina cin zarafin dalibai mata wadanda suka saka jihabi, domin gwamnati ta hore su da su daina.

Daga nan sai ya ci gaba da nasar da cewa batun saka hijabi ya na kotu, kuma su ne suka kai kara, maimakon a ce sun fito kan titi su na zanga-zanga, har a kai ga yi musu sharri ko yarfen su na daukar doka a hannun su.

Share.

game da Author