Jiya Laraba ne Jam’iyyar APC ta bayyana cewa ita fa ba za ta bi umarnin da Babbar Kotun Jihar Kwata ta yanke hukunci ba, inda ta kotun ta maida shugaban jam’iyyar da APC na jihar da uwar jam’iyyar ta kasa ta kora a kan shugabancin sa.
APC ta zargi Ishola Balogun-Fulani da yi wa jam’iyyar yankan-baya da zagon-kasa, a bisa zargin cewa ya na goyon bayan Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, wanda ya fice ya koma PDP.
Cire Ishola da ke da wuya, shi kuma sai ya garzaya Babbar Kotunn Jihar Kwara, ya maka APC kara a bisa rashin adalcin cire shi da aka yi ba bisa ka’ida ba.
An cire shugaban jam’iyyar ne na jihar Kwara shi da mukarraban sa, wato sauran shugabannin da ke rike da mukamai bayan Saraki ya koma PDP.
Ba nan kadai hukuncin ya tsaya ba, kotu ta kara jaddada cewa dan takarar gwamna na bangaren su Ishola Balogun shi ne halastaccen dan takara, ba dan takarar gwamna na daya bangaren APC na bayan su Oshimhole ba, wadda Bashir Bolarinwa ke jagoranta a jihar Kwara.
Kotun ta kuma umarci INEC ta amince da dantakar bangaren su Ishola Balogun, sannan ta yi watsi da na bangaren Bashir Bolarinwa, wato Abdulrazaq Abdulrahman.
Rahotanni sun ce Abdulrazaq zai daukaka kara, sai dai kuma ita uwar jam’iyyar APC ta ce ta na nan kan bakan ta na cewa ba ta amince da bangaren Ishola Balogunn ba, domin tuni ta kore su daga kan shugabanci.
Haka Kakakin APN, Lanre Issa-Onilu ya shaida wa PREMIUM TIMES a cikin wata takarda da ya fitar, ya ce hukuncin da kotun ta yanke, hukunci ne baubawan-burmi, wanda ba za su yarda da shi ba.
Discussion about this post