Awowi 48 bayan ragargaza garin Dan-Dambo, mahara sun kashe mutane 17 a Magami, jihar Zamfara

0

A wani sabon hari da mahara suka kai a kauyen Magami dake karamar hukumar Maradun, jihar Zamfara,akalla mutane 17 ne suka rasa rayukan su a wannan hari.

Kakakin rundunar ‘Yansandan jihar Mohammed Shehu bayyana wa manema labarai cewa akalla mutane 17 ne suka rasu a wannan hari da aka kai kauyen Magama.

Kakakin majalisar jihar wanda shine ke rike da kujerar gwamnan jihar, a rashin gwamna AbdulAziz Yari, Sanusi Rikiji ya jajenta wa yan uwan wadanda suka rasu sannan ya ce tune har ana aika karin jami’an tsaro zuwa wannan yanki.

Sarkin Maradun Muhammed Tambari ya yi kira ga gwamnati da ta tausaya wa mutanen jihar, su karo yawan jami’an tsaro yankuna Maradun.

Idan ba a manta ba Mahara dauke da makamai sun far wa kauyen Dan-Dambo dake karamar hukumar Birnin Magaji, jihar Zamfara inda a wannan karon har lalata da matan mutane suka yi da karfin tsiya.

Wani mazaunin kauyen Dan-Dambo ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa maharan sun far wa kauyen ne da misalin karfe 8 na daren Juma’a.

” Muna zaune ne kawai sai muka ji harbe-harbe ta ko-ina. Daga nan ne fa kowa ya fara gudun tsira. Mata ko da aka bari a gida wasun su sun sha dukan tsiya.

” Da zarar sun tambayeki ina kudi yake, idan kika ce babu sai su hau dukan mace. Wasu an ce har lalata sun yi da wasu matan.

” A haka ne fa suka rika kwashe tumakai da dabbobin da mutane suka mallaka. Sannan suka farfasa rumbuna suna dibar abinci.

Da suka gama abinda zasu yi sai suka kona inda suka fito.

Bayanai sun nuna cewa wasu da dama da suka gudu musamman mazaje sun gano iyalan su ne a kauyen Nasarawa Godal dake kusa dasu in da suka tafi neman mafaka.

Kamar yadda mazaunin ya bayyana, ya kara da cewa yanzu haka garin Birnin Magaji ne kawai yake da tsaro, shima wai don nan ne mahaifar ministan tsaro Mansir Dan-Ali.

Shi kuma ministan tsaro Mansur Dan Ali cewa yayi wai jihar Zamfara ya fada cikin matsalar rashin tsaro ne a dalilin rashin aikin yi da matasan jihar ke fama da shi, ta’ammali da kwayoyi da kuma gurguwar gwamnati da ake dasgi a jihar.

Share.

game da Author