Dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyar PDP, Atiku Abubakar, ya yi alkawarin bai wa mata manyan mukamai idan suka taimaka ya ci zaben shugaban kasa da za a gudanar cikin Farairu, 2019.
Atiku ya yi wannan alkawarin a Abuja, lokacin da ya ke ganawa da wata babbar tawagar mata.
Ya ce ya yi tunanin zaman musamman din ne domin ganawa da mata, saboda tun farkon kafa jam’iyyar PDP ba ta taba kin kare al’amurran mata ba.
“Tunda dai yawan ku ya kai kashi 50 bisa 100 na al’ummar kasar nan, to zan ba ku wakilci daidai da yadda zai dace da yawan ku.”
Ya ce wasu na jayayya da tantamar cewa ba za a iya cimma daidaiton rabon mukamai da mata a kasar nan ba.
Sai Atiku ya ce amma shi ya na ganin hakan ba gaskiya ba ne, domin ai jam’iyyar PDP ta dauko hanyar yin haka din, har sai da APC ta kafa gwamnati ne sannan aka ture su a baya.
“Ina tabbatar da daukar alkawari a gaban ku cewa idan na ci zabe zan shigar da mata a cikin manyan mukamai. Kuma dama idan za a iya tunawa, ko lokacin da ina Mataimakin Shugaban Kasa, sai da na shigar da kwararrun matan da suke da gogewar iya aiki a cikin gwamnati.”