Atiku ba dan asalin kasar Wurno bane, shirga wa mutanen Sokoto karya yayi – Murtala Wurno

0

Wasu daga cikin ‘yan asalin kasar Wurno dake jihar Sokoto sun karyata maganar tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar na cewa da yayi wai iyayen sa na da asali daga kasar Wurno.

Shugaban kungiyar manoma Tafarnuwa, da shinkafa na karamar hukumar Wurno Murtala Wurno da Kabiru Wurno sun karyata wannan zance inda suka kara da cewa Atiku yayi haka don neman yabo da siyasa kawai.

” A Kasar Wurno ne aka haifi sarkin musulmi na farko wato dan marigayi Usman Danfodio, Muhammadu Bello. Bai kamata Atiku ya shirga wa ‘yan Najeriya irin wannan karya ba da rana tsaka wai shi dan wannan yanki ne.

” Muna kira ga Atiku da ya maida hankalin sa wajen fadin gaskiya da tarerayar mutane a siyasar sa ba wai shirga karya ba don neman jama’a.

Idan ba a manta ba Atiku ya shela wa taron ‘yan jam’iyyar PDP a garin Sokoto cewa iyayen sa ‘yan asalalin kasar Wurno ne.

Share.

game da Author