An yi wa yara 102,403 allurar rigakafin cutar shan-Inna a jihar Kano

0

A yau Juma’a ne jami’in karamar hukumar Dala a jihar Kano Haruna Gunduwawa ya bayana cewa gwamnati ta samu nasarar yi wa yara 102,403 allurar rigakafin cutar shan inna zuwa yanzu.

Ya ce an yi wa yara masu shekara daya zuwa biyar a karamar hukumar.

Gunduwawa ya ce wannan karon an samu hadin kan iyaye wajen yi wa ‘ya’yan su allurar.

A karshe Jami’an hukumar cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko na jihar Aishatu Sani ta jinjina kokarin da karamar hukumar Dala, sarakunan gargajiya da kungiyoyin bada tallafi suka yi domin ganin an yi wa yara allurar rigakafin cutar shan Inna kyauta.

” Hadin kan da muka samu wajen iyaye ya nuna amincewar da mutane suka yi da yi wa ‘ya’yan su rigakafi.” Inji Aisha

Share.

game da Author