An yi garkuwa da dan takarar Majalisar Dokoki a Jihar Nasarawa

0

Rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa ta tabbatar da sace dan takarar Majalisar Jiha na Jam’iyyar APC, mai suna David Ayele.

Ayele ya na takarar wakiltar Karamar Hukumar Obi II a zaben 2019 mai zuwa.

Kakakin ‘yan sandan Jihar Nasarawa, Kennedy Idirisu, ya bayyana wa manema labarai a Lafia, babban birnin jihar cewa wasu ‘yan bindiga ne suka dirar wa Ayele a gidan sa da ke Tudun Kauri, wajen karfe 8 na dare a ranar Lahadi.

Idirisu ya ce ‘yan sanda sun amsa kiran neman daukin da aka yi musu cikin gaggawa, inda suka bi sawun masu garkuwar, kuma suka samu motar sa an ajiye ta a kan titin Obi zuwa Awe.

Ya ce su na kokarin ganin sun ceto wanda aka yi garkuwar da shi a cikin koshin lafiya, kuma za su magance matsalar garkuwa da mutane a fadin jihar.

Share.

game da Author