An kashe mutane 10 a harin Kaduna –‘Yan sanda

0

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna Yakubu Sabo ya bayyana cewa an kashe mutane 10 a kauyen Unguwan Pa Gwandara dake karamar hukumar Jema’a jihar Kaduna.

Sabo ya bayyana cewa wasu mahara ne suka kai wa wannan kauye hari da karfe 9:30 na yammacin Lahadi yayin da mazauna kauyen ke taron buki.

” A dalilin haka mutane goma suka mutu sannan da dama sun sami rauni.

Sabo yace rundunar ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro a jihar za su tabbata an kamo wadanda suka aikata wannan mummunar ta’asa.

A sakon jaje da gwamna Nasir El-Rufai ya aika wa mutanen wannan yanki, ya yi tir da wannan hari sannan ya umarci ‘yan sanda da su kamo wadanda suka aikata haka.

Ya kuma umurci karamar hukumar Jema’a da hukumar bada agajin gaggawa da su kai wa mutanen da abin ya shafa tallafi.

Share.

game da Author