An kama ‘yan sanda hudu bisa zargin su da ake yi da laifin fashi da makami, inda suka yi wa wani mai suna Theodore Ifunaya fashin Saifa 350,000, kwatankwacin naira 221,508.
‘Yan sandan su hudu su na aiki ne a Ofishin ‘yan sanda da ke Ijanikin a Lagos.
Kakakin Rundunar Jihar Lagos mai suna Chike Oti, ta tabbatar da cewa wanda aka yi wa fashin wani dan Najeriya ne mazaunin kasar Togo, kuma an kama wadanda suka yi masa fashin.
Ya ce idan aka tabbatar da laifin a kan su, za a kore su ne gaba daya sannan kuma za a hukunta su.
Sai dai kuma ya karyata zargin da ake yi cewa ‘yan sandan sai da suka yi wa wanda suka yi fashin tsirara, kamar yadda wasu suka rika yadawa.
Ya ce an tura su sashen binciken laifukan ‘yan sanda.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa ‘yan sandan su hudu sun yi wa wanda suka yi wa fashin kwanton-bauna ne, lkacin da suka gano cewa matafiyi ne daga kasar Togo, ya dawo gida domin yin hutun Kirsimeti.
Sun yhi zargin akwai kudi a hanun sa, a lokacin da ya shigo Najeriya ta kan iyakar Iyana-Ira a Badagry.
An bada rahoton cewa sun azabtar dac shi sannan kuma suka gano cewa ashe ma ya na dauke da kudi masu kauri tare da shi.
Sun jefa shi cikin motar su ta sintiri bayan sun lakada masa duka, sannan suka tafi da shi ofishin su, inda suka kwashe kudaden sa, sannan kuma suka aika aka kira wani dan canji, ya canji kudaden gaba daya daga saifa, ya bai wa ‘yan sandan nairori.
Sin yi wa wanda suka yi wa fashin barazana, sannan kuma suka ba shi naira 2000 suka ce ya hau mota zuwa gidan sa a Lagos.
Bayan da ya isa gida, ya bada labarin abin da ya faru da shi, ina nan take iyalan sa suka je suka shigar da rahoto a gaban Kwamandan Area ‘K’, Hope Akapor.
Okapor, wanda Mataimakin Kwamishinan ‘Yan sanda ne, ya sa an kamo su, kuma ya karbo masa kudin sa daga hannun su.
Za a gurfanar da su bada dadewa ba.
Discussion about this post