An gano sabuwar hanyar sanin cutar dajin da ke kama mahaifar mata kafin ya mamaye jiki

0

Kungiyar likitoci mai suna ‘American Cancer Society (ACS) ta gano hanyar yin gwajin jini domin gano cutar dajin dake kama mahaifan mace da wuri.

Likitocin sun bayyana cewa ana iya gano wannan cuta ce ta hanyar yin gwajin jinin da amfani da sinadarin ‘CA-125’.

Bisa ga bayanan su likitocin sun ce sun gudanar da wannan bincike ne domin kawar da matsalar rashin gane cutar da wuri.

” Cutar dajin dake kama mahaifa cuta ce dake yawan kama mata sannan da dama basu sani sai cutar ta mamaye jikin mace.

Likitocin sun kuma bayyana cewa sinadarin ‘CA-125’ na taimakawa wajen kawar da wasu matsalolin da ake kamuwa da su a lokacin da mace ke da ciki,kaban ciki,laulayin haila,Hepatitis da sauran su.

Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne wasu likitoci a jami’ar Harvard dake Boston kasar Amurka suka bayyana cewa shan maganin ‘Aspirin’ na kare mace daga kamuwa da cutar dajin dake kama mahaifa.

Likitocin sun gano haka ne a bincike da suka gudanar inda suka gano cewa mace kan samu kariya idan ta na shan wannan maganin kasa da yawan da ya kamata a sha.

Dama likita kan bada Izinin a sha miligaram 325 na wannan maganin amma samun kariya daga wannan cutar shine idan an sha miligaram 100.

” Bisa ga binciken da suka gudanar matan da suka sha miligaram 100 na wannan maganin sun samu kashi 23 bisa 100 na kariya daga kamuwa da wannan cutar fiye da matan da basu sha wannan magani kwata-kwata ba.

Share.

game da Author