An dawo da zaman lafiya a yankin da ’yan bindiga suka kai hari a Zamfara -’Yan sanda

0

Rundunar ‘Yan sandan Jihar Zamfara ta bayyana cewa ta maido da zaman lafiya a kauyen Dogon Maje, cikin Karamar Hukumar Tsafe, inda ‘yan bindiga suka kai mummunan hari.

Kakakin Yada Labarai na ‘yan sandan jihar ya ce zaman lafiya ya sake wanzuwa a kauyen, kuma nan gaba za a sanar da cikakken abin da ya faru, da zarar jami’an da aka tura kauyen sun dawo da bayanan da suka binciko.

Duk da haka ya tabbatar da cewa an kashe rayuka a harin da masu dauke da bindigogi suka kai, amma bai iyakance ko kiyasta yawan wadanda suka rasa rayukan na su ba.

Kamfanin Dillancin Labarai NAN, ya ruwaito cewa mai yiwuwa mahara sun kai hari a kauyen ne domin yin ramuwar-gayyar kashe wasu mata uku da aka yi a yankin, a cikin makon da ya gabata.

NAN ta kuma ji cewa masu harin sun dira kauyen ne a ranar Juma’a wajen karfe 10:30 na dare, inda take suka bude wuta.

Wani mai suna Rayyahi Abubakar, ya shaida cewa an kashe mahaifin sa mai suna Ibrahim Kuryan-Madaro kuma suka cire kan sa daga gangar jikin.

Rayyahi ya ce mahaifin sa malamin addinin musulunci ne, kuma ya je garin ne domin amsa wata gayyata da aka yi masa.

Ya ce, “Daya daga cikin ‘yan bindigar ya kira ni ta wayar mahaifi na, ya ce min mun kashe uban ka, gobe ka zo Dogon Maje ka dauki gawar sa.”

Ya ce an rufe gawar mahaifin na sa a Zawiyya, cikin Gusau a ranar Asabar.

Share.

game da Author