Dillalan man fetur a fadin kasar nan sun bai wa gwamnatin tarayya wa’adin kwanaki bakwai cewa a biya su bashin naira bilyan 800 da suke bi, ko kuma su hana gudanar da aikin dauka da rarraba man fetur a dukkan daffo da ake tara mai a kasar nan.
Duk da cewa kamfanin NNPC shi kadai ne ke shigo da man fatur tattace a cikin kasar nan, amma kuma NNPC din ta dogara ne da wuraren adana fetur na manyan ‘yan kasuwar fetur domin ajiyewa da kuma raba man.
Matsawar aka rufe manya-manyan rumbunan ajiyar man, to Najeriya za ta sake afkawa cikin wani sabon matsanancin wahalar man fetur, kamar wanda ta fada a cikin watan Disamba na shekarar da ta gabata.
Wadannan gungunn gamayyar ‘yan kasuwa, sun hada da ‘Major Oil Marketers Association of Nigeria (MOMAN), sai kuma DAPPMA wato kungiyar masu manyan rumbunan tarawa da adana man fetur, da Independent Petroleum Products Importers, wato IPPIs.
Dukkan wadannan kungiyoyi sun yi taro jiya Lahadi a Lagos, inda suka bayar da sanarwar cewa idan gwamnati ba ta biya su kudaden su naira bilyan 800 nan da kwanaki 7 ba, to duk za su sallami ma’aikatan da ke aiki a wuraren adanawa da rarraba man fetur din.
Da ya ke tabbatar da wannan bayani ga Kamfanin Dillancin Labarai, NAN, Patrick Etim na IPPI, ya ce abin takaici su ma wadannan kamfanonin duk bankuna sun kwace musu kadarori, saboda kasa biyan basukan da bankunan ke bin su.
Don haka ya ce wannan ce kadai mafita a gare su, tunda su ma su na bin gwamnatin tarayya makudan kudade, gara ta gaggauta biyan su.
Ya ce gara su sallami ma’aikatan su kowa ya zauna gida ya jira albashi da kudaden ariyas da su ke bi a duk lokacin da gwamnati ta biya kamfanonin hada-hadar mai din kudaden su na tallafin mai har naira bilyan 800.
Ya ce watanni da dama kenan ana sa-toka-sa-katsi da gwamanti, amma kullum alkawarin yau daban, na gobe ma daban.