Tun bayan sauya sheka da sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya yayi zuwa jam’iyyar PRP, jam’iyyar ta karade jihar Kaduna, lungu lungu, sako-sako, kwararo-kwararo.
Hakan kuwa na da nasaba da irin namijin kokarin da sanatan yake yi wajen ganin ya tallata jam’iyyar a jihar ta inda za ta yi tasiri ganin shine dan takarar jam’iyyar a zaben sanata mai zuwa.
Shehu Sani dai ya koma PRP duk da zawarcin sa da jam’iyyar PDP ta yi ta yi masa a lokacin da wasu da dama ke ganin yana cikin ayarin sanatocin da ke kokarin canja sheka a wancan lokaci. Sai dai kuma daya ke sanata Shehu mutum ne mai akidar Talakawa da ci gaban al’umma sai ya ga ya fi dacewa ne ya koma PRP da kowa ya sani jam’iyya ce mai muradin Talaka da marasa galihu.
Tun a lokacin da yake APC, sanata Shehu Sani yayi wa tafiyar sa take ” Jagorar Rundunar Talakawa” da hakan ya ke nufin cewa talakawa ne a gaban sa.
Masu yin fashin baka a siyasar Kaduna ta tsakiya sun bayyana cewa akwai yiwuwar za a iya samun akasi a sakamakon zaben sanata a shekara mai zuwa domin kuwa jam’iyyun da za su fafata ba su kai jam’iyyar PRP zama kusanta da talakawa ba sannan da mutane a kwanakin nan ba a yankin Kaduna ta Tsakiya.
” Sanata Shehu Sani ya taka rawar gani a majalisar dattawa kuma abin alfahari ne ga duk wani mazaunin yankin Kaduna ta tsakiya domin idan har za ka ambato sanatoci 10 cikin sama da 100 dake majalisa dole ka ambato sanata Shehu Sani. Idan bai zo na uku ba zai zama na hudu tabbas.
” Kowa ya san irin gudunmawar da ya bada wajen fallasa badakalar kwangilar cire ciyawa da yayi sanadiyyar rasa aiki da sakataren gwamnatin tarayya a wancan lokacin Babachir Lawal yayi. Sannan kuma duk da haka bai tsaya ba wajen fadi wa gwamnati gaskiya idan hakan ya kama.
” Yayi kokarin ganin ya ci gaba da zama a inuwar jam’iyya daya da shugaba Buhari amma hakan bai yiwu ba da ya sa dole ya canja sheka zuwa jam’iyya da take mai kama da halin Buhari, wato PRP.” Inji Lawan Inusa, wani fitaccen dan kasuwa a garin Kaduna da yake zantawa da PREMIUM TIMES HAUSA.
A Jihar Kaduna ba a taba takara musamman mai neman Kujerar sanata ko na majalisar Kasa da yake irin Kamfen na bin jama’a gida-gida da wuraren sana’ar su domin daraja su da neman goyon bayan su kamar yadda kwamared Shehu Sani ya ke yi a wannan lokaci.
Sai dai ba za ayi tuya ba a manta da albasa, akwai aiki matuka a gaban sa domin dan takarar kujerar a APC wato Uba Sani shima fa ba kanwan lasa bane. Bayan fice da yayi a harkar siyasa sannan kuma akwai yiwuwar farin jinin Buhari yayi masa tasiri a zaben tunda rana daya za a yi.
Akwai Lawal Adamu na jam’iyyar PDP da akayi wa lakabi da yaro dan siyasa mai tashe, Shima fa ya kunnu kai matuka yana zuba kamfen yadda ya kamata.
Jama’a da dama a Kaduna ta tsakiya sun fara karkata ne zuwa ga jam’iyyar PRP saboda Jagorar rundunar Talakawa ya mike tsaye don ganin shine ya yi nasara a zaben 2019 din. Mutane da dama suna ganin matsalolin da Shehu Sani ya samu ba da Talakawa bane da ‘yan siyasa ne, saboda haka su dai ga gwanin su
Discussion about this post