Ainihin dalilin da ya sa Akbabio da Obanikoro suka sauya sheka zuwa APC daga PDP – Sule Lamido

0

Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido ya bayyana cewa babban dalilin da ya sa wasu daga cikin jiga-jigan ‘yan jam’iyyar PDP kamar su Godswill Akpabio da Musliu Obanikoro shine don jam’iyyar na neman ta shi mutuncin su da garfin gwmamnati.

” Tun da gwamnati ta kyalla ta hango irin kudaden da wadannan mutane suka mallaka a asusun ajiyar su na banki sai suka yi amfani da EFCC suka fara bibiyan su sau da kafa. Daga nan sai suka rika ce musu ko su dawo jam’iyyar APC a yafe musu ko kuma su ci gaba da zama a PDP ayi musu tonon silili sannan a daure su.

Lamido ya ce wannan shine ainihin dalilin da ya sa mutane kamar su Akpabio da Obanikoro suka ga ba za su iya jurewa cin mutuncin ba suka fice daga PDP din.

” Jam’iyyar APC ta yi amfani da bakin talauci da ta saka ‘yan Najeriya a ciki tana bin abokanan adawar tana bugewa da karfin tsiya. Ko kuma ka dawo jam’iyyar APC a yafe maka.

Wannan maganganu dai Lamido yayi su ne da yake bada jawabi a filin taron kaddamar da kamfen din jam’iyyar PDP a jihar Jigawa.

Bayannan ya roki wadanda suka canja sheka, wato suka fice daga PDP zuwa APC a dan kwanakinnan da su dawo jam’iyyar PDP.

Share.

game da Author