Gwamnatin Jihar Akwa-Ibom ta bayyana dalilin ta na hana Shugaba Muhammadu Buhari yin amfani da Babban Filin wasa na Uyo, a ranar Juma’a ta sama.
Jam’iyyar APC ta nemi a ba ta izinin yin amfani da filin wurin taron gangamin yakin neman zaben ta a jihar.
Sai dai kuma ita gwamnatin jihar ta maida wa APC amsa cewa ta dai yi amfani da karamin filin kwallon garin Uyo, wanda ba shi ne babba na kasa da kasa ba.
Karamin filin dai ya na da kujeru 30,000 ne.
Kwamishinan Wasannin Jihar, Monday Uko ya ce dalilin hana APC da Buhari yin taro a filin shi ne, saboda za a fara kakar wasannin Premier na Najeriya a ranar 13 Ga Janairu, 2019, kuma a filin ne Akwa United za su rika yin dukkan wasannin su na gida.
Ya ce idan aka tattake ciyawar filin a wurin taron APC, to ba yadda za a yi a sake shuka waya ciyawar har ta fito a cikin ‘yan kwanaki bayan yin taron na APC.
“Sannan kuma kamfanin Julius Berger, wanda shi ne ke kula da ciyawar, ya bada shawara cewa a lookacin hunturu kada a sake a yi wata didima a cikin ciyawar filin, idan dai ba wasan kwallo ba ne.”Inji Uko.
Ya kara da cewa ya zama dole ya fito ya yi wannan bayani domin wasu manyan ‘yan jagaliyar siyasa a jihar Akwa Ibom har sun fara yin mummunar fassara kuma sun fara yarfe.
Discussion about this post