A wancakalar da Buhari a 2019 kawai, shine farinciki na – Inji Obasanjo

0

Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ya karyata rade-radin da ake ta yadawa wai yanzu baya mara wa ko wani dantakara baya a zaben 2019, cewa wai kowa ma ya yi nasara a zaben.

Obasanjo ya karyata haka inda ya kara da cewa shi bai fadi haka.

A sanarwar haka da ya fito daga bakin kakakin sa Kehinde Akinyemi, Obasanjo ya ce yananan kan bakan sa na lallai burin sa shine yaga an wancakalar da Buhari a 2019.

” Jawabin da Obasanjo yayi a wajen taron Iwo, bai ce wai ga wanda za a zaba ba ko kuma wani abu game da dantakarar da ya karkata ga. Obasanjo kira yayi da mutane su zabi wadanda za su inganta rayukansu ne fiye da yadda yake a yanzu.

” Duk da kokari da yayi na kada ya sakala siyasa a wajen wannan taro sai da wasu suka kulla wannan zance na karya.

Obasanjo ba ya tare da wannan gwamnati a dalilin gazawa da tayi wajen inganta rayukan mutanen kasa, samar da tsaro, bunkasa tattalin arzikin kasa da sauran su.

Sannan yayi kira ga ‘yan Najeriya da su yi wa kan su adalci wajen zabin wadanda zasu inganta rayukan su ba wadanda zasu saka su cikin kangin rayuwa ba.

Share.

game da Author