2019: Yadda santsin siyasa ya kayar da ministocin Buhari

0

Fitowa neman takara ko shiga zaben fidda gwanin siyasa, tamkar cinikin biri ne ya na saman bishiya. Idan ba a tarba maka ka kama ba, ko kuma an samu wani baushi gwanin harbi ya rikito maka shi kasa ba, to biri bai zama na ka ba.

Shi kuwa Bahaushe da ya ke ya san fari da bakin siyasa, kuma ya san hairi da sharrin ta, sai ya ke mata kirari da: Siyasa romon jaba, ga kitse ga wari!

Daga cikin dubban ‘yan siyasar da suka fito takarar zabukan fidda gwani a jam’iyyun siyasa daban-daban, akwai ministocin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari su shida.

Duk da cewa Buhari ya albarkaci takarar su da kuma nuna amincewa da su, hakan bai kais u ga nasarar fitowa wakilan jam’iyyar APC a zabukan 2019 mai zuwa ba.

Ko dai an nuna musu tuggun siyasa ko kuma an nuna musu cewa su kananan ‘yan jagaliya ne, wadanda tsoffin ‘yan alewa da sabbin yanka rake suka yi musu tadiya, santsin siyasa ko talalabiya ta kwashe su, ta rumtuna su da kasa.

Daga cikin ministocin Buhari shida, daya ne kawai ya sha da kyar, har ya samu takarar zaben 2019 a karkashin jam’iyyar APC.

KAYODE FAYEMI SHUKA GYADAR-DOGO

Ministan Harkokin Ma’adinai, Kayode Fayemi ne kadai wanda ya tsallake siradin santsin siyasa. Fayemi ya sauka daga minista, ya tsaya takarar zaben gwamnan jihar Ekiti, kuma ya yi nasara.

Dama a baya ya taba yin gwamna a Ekiti, amma Ayo Fayose ya kayar da shi a zaben gwamna, inda shi ma a lokacin Fayose din ya koma a karo na biyu a 2014.

A yanzu dai Fayemi gwamna na a karo na biyu. Shin kam siyasa ta yi masa gyadar-dogo, sama ‘ya’ya, kasa ma ‘ya’ya.

MAMA TARABA TA YI JIFAR-GAFIYAR-BAIDU

Aisha Alhassan, tsohuwar Ministar Harkokin Mata da Adebayo Shittu, Ministan Harkokin Sadarwa, ba su samu nasara a zaben fidda-gwanin jam’iyyar APC ba. Tun a wurin tantance sunayen ‘yan takara ne shugabannin jam’iyyar APC suka ki tantance su.

Ita Mama Taraba, takarar gwamnan jihar Taraba ta nema, kamar yadda ta fito a zaben 2014, a karkashin jam’iyyar APC, amma ba ta yi nasara ba.

Shi kuma Adebayo Shittu, ya so tsayawa takara ne ta gwamnan jihar Oyo.

APC ta soke takarar Mama Taraba saboda kusancin ta ga dan takarar shugabancin kasa a karkashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar.

Tun a cikin 2017 Aisha ta fito ta nuna wa duniya cewa ita fa har yanzu ta na da muba’iya ga ubangidan siyasar ta, Atiku Abubakar.

Alhassan ta yi wannan kalami ne a lokacin da ta ke kan mukamin minista, a karkashi gwamnaatin Buhari.

Shi kuwa shugaban APC Adams Oshimhole, ya nuna cewa zai yi maganin ta, kuma shi ba shi da hakuri kamar Buhari.
Wancakali da APC ta yi a wurin tantance ‘yan takarar APC na gwamnan jihar Taraba, sai ta fice daga jam’iyyar ta koma UDP.

RAMUWAR GAYYAR MAMA TARABA A KAN APC

Ba ta dade da ficewa daga jam’iyyar APC ba, sai Mama Taraba ta kwashi motocin daukar kaya cike da karti, ta dumfari sakateriyar APC ta jihar Taraba, da ke Jalingo a fusace.

A cikin hasala ta sa aka kwashi duk wani abu mai amfani a cikin ofisoshin sakateriyar. An kwashi tebura, kujeru, firji, da duk wani abin amfani daga kayan bukatun aikin ofishin APC aka watsa cikin motocin da ta je da su. Ganau ba jiyau ba ya hatta labulaye ba ta bari ba, sai ta ta tsinke su, ta yi gaba da su.

Jummai, wadda aka fi sani da Mama Taraba, ta shaida wa manema labarai cewa duk it ace ta sayi kayayyakin da kudaden ta. Don haka a cewar ta, ba za ta raka asara da guda ba, tunda an hana ta takara, kuma ta fice daga jam’iyyar ba.

ADEBAYO SHITTU: BAKI SHI KE YANKA WUYA

Shi kuwa Minista Adebayo Shittu, shi da kan sa a baya a tabbatar da cewa bai je aikin Bautar Kasa ba, bayan da ya kammala dirigi din sa na farko.

Ya amince da haka ne bayan PREMIUM TIES ta fallasa cewa shi ma Shittu kamar tsohuwar minista Kemi Adeosun, bai je aikin bautar kasa ba, wato NYSC.

Fitowar labarin ke da wuya, sai ya ce tabbatas bai je aikin bautar kasa a shekarar 1979 da ya kammala kartun digiri din sa na jami’a ba.

Shittu ya kafa alilin cewa bai je bautar kasa ba, saboda a shekarar ne kuma ya shiga takarar zaben dan majalisar jihar Oyo kuma ya yi nasara.

A na sa tawilin, Shittu ya ce shi a zaton sa, wancan aiki da ya yi na dan majalisa duk ya shafe rashin zuwan sa aikin bautar kasa.

Sai da kuma shi shugaban APC, adams Oshimhole ya ce kowa ya san kin zuwa aikin bautar kasa, babban laifi ne, kuma akwai dokar da ta hana ma dauki ma’aikaci in dai har bai je aikin bautar kasa ba.

MUSTAPHA SHEHURI: SAKI RESHE KAMA GANYE

Ya na zaman sa a matsayin Karamin Ministan Ayyuka, Makamashi da Gidaje, ya ajiye mukamin sa ya shiga neman takarar gwamnan jihar Barno a karkashin APC.

Ganin cewa ya na Ministan Buhari, ya shiga takarar zaben fidda gwani a cikin zaratan masu takara 31.

Ana kusa da zaben fidda gwani sai masu takara 21 suka janye, suka bar wa Babagana Umara-Zullum.

Yayin da aka fafata takara tsakanin Zullum da sauran ‘yan takara goma da ba su janye ba, ciki har da Shehuri, Zullum ya samu kuri’u 4,432, shi kuma Shehuri guda 1 kacal. Wannan fa shi ne Hausawa ke cewa haihuwa daya horon tukiri.

Shehuri ya ji ciwon kayen da aka yi masa. Duk da cewa akwai wasu ‘yan takarar da suka samu kuri’u kudan 20, ba su korafi da raki kamar Shehuri ba.

Domin shi har manema labarai ya tara, ya bayyana ceea an yi magudi, rashin adalci da kuma fashin ‘yancin jama’a da rana tsakar rana.

Shehuri ya ji zafin kaye sosai, ya yi kuka, ya yi kururuwa, ya yi bobbotai. Kai irin yadda ya rika furta bakaken kalamai a gaban manema labarai, ba zai rasa yin Allah ya isa a zuciyar ba, idan har bai yi a sarari ba.

MANSUR DAN-ALI: NEMAN RUWA A HAMADA

Ministan Tsaro Mansir Dan-Ali ya nemi tsayawa takarar zaben gwamna a jihar Zamafara.

Tashin farko al’ummar jihar ba su yi na’am da shi ba, saboda duk da cewa ya na dan asalin jihar Zamfara, kuma ministan tsaro sunkutukum, bai tabuka abin kirki wajen mamayar da mahara, makasa kuma masu garkuwa da jama’a suka yi wa jihar Zamfara ba.

A farkon dawowar mulkin farar hura a 1999, Zamfara ta yi suna a duniya, saboda kaddamar da Shari’ar Musulunci da aka yi a jihar.

A yanzu kuma jihar Zamfara ta yi kaurin suna a duniya, saboda yadda masu samame suka mamaye jihar, ta yadda al’ummar jihar sun shiga cikin mawuyacin halin kisa, sata, fashi da garkuwa da mutane.

Rikicin zaben fidda gwanin da ya dabaibaye jihar Zamfara ya sa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC haramta wa jihar Zamfara zaben 2019.

UGURU USANI

Shi ne Ministan Kula da Harkokin Neja Delta. Buhari ya sa masa albarkar tafiya neman takarar gwamna a jihar Cross Rivers.

Sai dai kuma Uguru ya sha gurgura a hannun abokin takarar sa, Sanata John Owan-Enoh, wanda ya samu kuri’u 82, 227, shi kuma Uguru aka gurgura masa kuri’un hana-rantsuwa guda 1,437.

DA SAURAN RINA A KABA

Masu hangen nesan siyasa na ganin cewa wadannan ministoci da aka kayar a zaben fidda-gwani, ba za su zage damtse wajen ganin APC ta samu gagarimar nasara a jihar su ba, musamman a zabukan mukaman da aka kayar da su.

Wasu ma na ganin cewa hatta a zaben shugaban kasa ba za su yi gumi har su yarfe domin ganin Buhari ya yi tazarce ba. Domin sun san ko ma APC ta sake samun nasara, to da wuya a sake tafiya tare da su a matsayin ministoci, mukaman da suka raina har suka jaraba neman gwamna.

Share.

game da Author