2019: ‘Siradin’ da zai yi wa Shugaban APC, Adams Oshimhole wuyar tsallakewa

0

Shugaban Jam’iyyar APC Adams Oahimhole na fama da matsananciyar rashin jituwa tsakanin sa da wasu gwamnonin jam’iyyar da ya ke shugabanci, bayan mummunan sabanin ya dagula jam’iyyar sakamakon zabukan fidda-gwani, wanda gwamnonin suka zargi su Oshimhole da yin tuggun kin fito da dan takarar da suke goyon baya.

Wannan sabani ya faru a jihohin da APC ke mulki, inda kuma gwamnonin za su kammala wa’adin su na shekaru takwas, ba za su sake tsayawa takarar gwamna ba. Amma banda jihar Ondo.

Jihohin sun hada da Imo, Ogun, Zamfara da kuma Ondo.

Cikin Nuwamba, DSS sun gayyaci Oshimhole inda suka yi masa tambayoyi dangane da zargin sa da wasu gwmnoni suka yi cewa ya karbi kudade masu tarin yawa ya baddala sakamakon zaben fidda-gwani a jihohi da dama.

Abdulaziz Yari bai ji dadin yadda sakamakon zaben fidda gwani ya kasance a jihar Zamfara ba. A karshe ya haifar da rudanin da ta kai INEC ta haramta wa APC tsayawa takara a jihar Zamfara. Amma dai maganar ta na kotu zuwa yanzu.

Ibikunle Amosun na jihar Ogun ya rika fesa wa Okorocha, Tinubu da Bode George ruwan bakaken maganganu, a bisa zargin su da daure gindi aka bai wa INEC sunan Dapo Abiodun a matsayin dan takarar gwamna, maimakon sunan Adekunle Akinbiyi, wanda gwamnan ke goyon baya.

Gwamna ya goyi bayan Adekunle komawa wata jam’iyya, kuma ya na yayata ceea ba zai goyi bayan dan takarar APC a zaben gwamnan jihar.

Share.

game da Author