2019: Gwamnonin APC sun bijere wa taron da Oshiomhole ya yi da ‘yan takarar gwamna na APC

0

Akasarin gwamnonin jam’iyyar APC mai mulki, sun yi watsi daga halartar taron ganawar da shugaban jam’iyyar, Adams Oshiomhole ya shirya yi tare da dukkan ‘yan takarar gwamna na APC a kasa baki daya.

Oshiomhole ya shirya ganawar ‘yan takarar ne tare da shi da kuma Mambobin Kwamitin Zartaswa na APC.

Oshiomhole ya ce ya na sa ran halartar ‘yan takarar gwamna daga jihohi 20 da kuma gwamnoni tara daga jihohi daban-daban.

Ya ce ya kira taron ne domin a gana, kuma a san juna ido-da-ido.

Sai dai kuma wani abin lura, shi ne, gwamnoni biyu kacal suka halarci taron, su ne Sani Bello na jihar Neja da kuma Simon Lalong, na jihar Filato.

Sai dai kuma jam’iyyar APC ba ta ce komai ba game da rashin zuwan da gwamnonin suka yi.

An fara taron da misalin karfe 12:10 na rana, aka tashi bayan karfe 2 na yamma.

An kyale ‘yan jarida sun shiga sun ga yadda aka fara gudanar da taron.

A wurin taron an gargadi jigogi da manyan ‘yan jam’iyya kada su goyi bayan ‘yan takara na wasu jam’iyyu, sai dai na APC kawai.

Wannan gargadi ya zo ne a daidai bayan da gwamnan jihar Ogun, Ibekunke Amosun ya yi alkawrin cewa ba zai goyi bayan dan takarar gwamnan APC na jihar Ogun ba.

Haka shi ma Gwamnan Rochas Okorocha na jihar Imo, sirikin sa ya fice daga APC, ya koma AA, wadda ake da kyakkyawan zato cewa shi Okorocha zai mara wa baya.

Share.

game da Author