2019: Gwamna Okorocha ya ki halartar kamfen din APC a jihar Imo, Oshiomhole ya yaga masa riga

0

Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Adams Oshiomhole, ya jaddada cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya na goyon bayan dan takarar gwamnan jihar Imo Sanata Hope Uzodimma 100 bisa 100.

Ya bayyana haka jiya a Enugu a lokacin da APC ta kaddamar da kamfen da dan takarar gwamnan jihar a karkashin APC, wanda Okorocha ba ya goyon baya.

An samu sabani da Okorocha da uwar jam’iyyar APC ta kasa tun bayan hadin bakin da gwamnan ya yi zargi an yi an kayar da dan takarar da ya nemi ya gaje shi, kuma sirikin sa, Uche Nwosu.

A halin yanzu dai gwamna Okorocha ya na bayan Nwosu ne ba APC ba. Nwosu da magoya bayan sa sun koma jam’iyyar DPP.
Sai dai kuma har yanzu Okorocha ya na nan a APC inda ya tsaya takarar sanatan yankin su.

A wurin kamfen, Oshiomhole ya yi wa Okorocha kaca-kaca inda ya kira shi da magoya bayan sa batattu kuma ‘yan boge da ‘yan gangan.

Ya ci gaba da gwasale Okorocha, ya na nuna zamanin mulkin sa ba alheri ba ne a jihar Imo.

Ya kuma tunatar wa jama’a irin ragabzar da Okorocha ya rika yi a lokacin da ya ke gwamna, har ya tunatar da su wani furuci da aka yi ikirarin cewa gwamnan ne ya furta da bakin sa, inda ya ce jihar Imo ta na da kudin da za ta yi ayyuka, amma ba ta da kudin biyan ma’aikata albashi.

Oshiomhole ya shaida wa ma’aikata cewa Uzodimma ba zai yi wasa da albashin su ba, su ma sarakunan gargajiya zai martaba su kuma ya mutunta su, ba zai yi musu rikon-sakainar-kashi ba.

Ya ce al’ummar jihar Imo sun dandana bakin mulkin Okorocha na shekaru takwas, amma idan suka zabi Uzodimma, to sannan za su gane dadin canji da kuma karsashin mulkin dimokradiyya.

Sanata Uzodimma shi ne wanda Hukumar ICPC ta damke watanni biyu da suka gabata a filin jirgin saman Lagos, yayin da ya dawo daga wata tafiya da ya yi kasashen waje.

Ana zargin sa da karbar kwangilar aikin kwashe yashi a tashoshin jiragen ruwa, ya karbi bilyoyin nairori, amma ko mangala daya bai kwashe ba.

A yanzu dai shi ne dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar Imo.

Share.

game da Author