2019: Duk wanda ya taya ni sake cin zabe ba zai yi wahalar banza ba, zan saka masa – Buhari

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa magoya bayan sa alkawarin cewa a wannan karon zai saka wa duk wanda ya jajirce wajen biyayya da kuma aiki tukuru.

Buhari ya bayyana haka jiya Laraba a Abuja, a lokacin da ya ke gabatar da jawabi a wurin kaddamar da wata kungiyar goyon bayan sa mai suna “Together Nigeria”.

Buhari wanda ya nuna godiyar sa ga kungiyar, ya ce “wasu mutane da kungiyoyi na korafin mun yi watsi da su saboda mun kasa dadada wa kowa ran sa.

“Amma ina tabbatar muku da cewa a wannan karon, za mu saka wa wadanda suka nuna jajircewa da kuma biyayya matuka daidai gwargwado.”

Ya ce taron ya tunatar da shi irin dimbin goyon bayan da ya ke samu daga kungiyoyi daban-daban a tsawon shekaru da dama.

Da yawa su na korafi da gwamnatin Muhammadu Buhari da kuma shi kan sa Buhari, cewa sun sha wahalar ganin ya zama shugaban kasa a tsawon shekaru da dama su na tare da shi, amma bayan ya ci zabe, sai ya juya musu baya.

Wasu kuma sun zarge shi da bada wasu mukamai ga wadanda ba su yi masa wahalar komai ba, ciki kuwa har ma da wadanda suka yi fafutikar ganin sun kayar da shi zabe.

Baya ga wannan kuma, Buhari ya raba hanya da daruruwan wadanda suka fi cin kwakwa da shan wahalar tallar siyasar sat un daga farko har zuwa kusan lokacin da ya samu nasarar zama shugaban kasa a karon takarar sa ta hudu.

Da yawa wadanda ke tare da shugaban kasa a yanzu, wadanda a baya suka rika yi masa kafar ungulu ne wajen kawo masa cikas din yin nasara.

Da yawan masu adawa da shi kuma a yanzu, wadanda suka sha wahalar talllar sa ce da kudin su, da gumin su da kuma sadaukar da lokacin su.

Share.

game da Author