2019: Dalilai 5 da ya sa zaben Buhari ya wajabta ga ‘Yan Najeriya – Ribadu

0

Tsohon shugaban Hukumar EFCC, Nuhu Ribadu ya bayyana wa dubban magoya bayan sa a garin Yola cewa lallai shugaba Muhammadu Buhari ya cancanci zarcewa a karo na biyu domin ci gaba da ayyukan ci gaba da yake yi a kasar nan.

Ribadu ya ci gaba da cewa da ga wannan rana ta Litini, ya mika wa Kamfen din Buhari gaba daya motoci, ofisoshi da kayan aiki da yayi amfani da su a wajen neman takarar gwamnan jihar Adamawa da yayi an canja musu fasali da launi sun rikide na kamfen din Buhari.

Bayan haka ya zano wasu dalilai da ya ce hujjojine ga duk mai kaunar Buhari da ma ‘Yan Najeriya su sake zaban sa a karo na biyu musamman ga mutanen yankin Arewa maso Gabas.

1 – Zaben 2019, zabe ne da zai banbanta tsakuwa da aya. Zaben kauce wa irin fuskokin da suka rugurguza kasar nan a rungumi gwamnati mai adalci.

2 – Inganta wa da samar da tsaro mai nagarta kamar yadda ake dandanawa yanzu musamman a jihar Adamawa sauran yankunan kasarnan.

3 – Ayyukan ci gaba da ake samu a karkashin wannan gwamnati musamman a sassan jihar da ba a taba samun irin haka ba nuni ne cewa wannan gwamnati na da muradun ci gaban mutanen wannan jiha.

4 – Manoma suna ta kwankwadan romon shirin tallafi da gwamnatin tarayya ta ke ba su domin bunkasa ayyukan su.

5 – Yaki da cin hanci da rashawa da fatattakar barayi ya yi matukar tasiri a wannan kasa.

Share.

game da Author