2019: CAN ta ce a guji zaben ’yan ci-da-ceto da masu neman mukamai ido-rufe

0

Shugaban Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN), Sam Ayokunle, ya yi kira ga ‘yan Najeriya su guji zaben masu neman hawa mukaman mulki ido rufe.

Ya yi gargadin cewa a zabi ‘yan takara nagari, ba baragurbin ‘yan siyasa ba a zaben 2019.

Ayokunle ya yi wannan kira ne a lokacin da yake hira da manema labarai, bayan ganawar da ya yi da wasu ‘yan takarar shugaban kasa su 14, a Abuja, wadanda suka yi masa bayanin shirin da suke dauke da shi wajen ciyar da ‘yan Najeriya a gaba, da kuma tsarin da suka yi shirin yi wa coci-coci.

Ya ce coci ya yi tunanin ganawa da ‘yan takara domin ya ji irin abin da suka tsara wa al’ummar kasar nan da kuma irin cancantar da suke da ita wajen neman hawa babbar kujerar shugabancin Najeriya.

Ya ce daga yanzu coci ya daina yin shiru a irin wannan yanayi, saboda sai kasa ta inganta ta samu zaman lafiya shi ma cocin zai samu zaman lafiya da yalwa.

Ya ce idan har zaben 2019 bai kasance mai adalci kuma ingantacce, sahihi kuma karbabbe ba, to ‘yan Najariya za su shiga mawuyacin hali, kuma abin da ya ci Doma ba zai bar Awai ba.

Ma’anar sa, duk mawuyacin halin da kasar nan za ta shiga, to zai shafi coci-coci.
A karshe ya nuna matukar damuwar sa kan yadda wasu ‘yan siyasa ke hankokon cin zabe ko ta wane hali.

Ya kuma yi kira ga INEC, jami’an tsaro da sauran wadanda abin ya shafa, su tabbatar da sun bi ka’idar da dokoki suka shimfida a lokacin zaben 2019.

Share.

game da Author