Jam’iyyar APC a jihar Kaduna ta bayyana mambobin kwamitin kamfen din ta na zaben gwamna mai zuwa a jihar.
A cikin jerin wadannan sunaye akwai ministan Kudi Zainab Ahmed da shugaban Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa NPA, Hadiza Usman.
Sannan akwai tsohon dan takarar gwamnan jihar a jam’iyyar PDP Sani Bello da ya sauya sheka zuwa APC a makonnin da suka gabata.