Na amince a kafa dokar ko-ta-baci a Jihar Zamfara – Gwamna AbdulAziz Yari

0

Gwamnan jihar zamfara, Abdul Aziz Yari ya bayyana cewa shima ya amince a kafa dokar ko ta baci a Jihar ganin cewa ayyukan ta’addanci ya ki ci ya ki cinyewa a jihar.

Gwamna Yari ya fadi haka ne a garin Gusau bayan ya dawo daga kasar Saudiyya inda ya tafi aikin Umrah.

Yari ya ce jihar na bukatar zaman lafiya na dindindin idan hakan ba zai yiwu ba to duk yadda za a bi a samarwa mutane zaman lafiya ya na tare da wannan shiri.

” Da ace a matsayina na gwamna, doka ta bani damar in dauki bindiga don fafatawa da wadannan ‘yan ta’adda da na fito mun fafata.

” Wani abin takaici da ban haushi shine ganin cewa su kan su wadanda ake sace wa ko kuwa ayi garkuwa da, ‘Yan uwansu ne ke aikata hakan. Sai su sace su su lula da su cikin daji sannan su ne mi a biya diyyan su tukunna kafin su saki ‘yan uwan nasu. Darin haka ta ina za a faro.

” Dole ne fa sai mun hada kai dukkan mu a jihar sannan mu tona asirin wadanda muka sani suna aikata wannan abu, idan ba haka ba to ko ba za a iya kawo karshen wannan baka’ da ake fama da shi a jihar ba.

Yari ya yaba wa jami’an tsaro bisa ga kokarin da suke yi na samar da tasro a jihar.

Share.

game da Author