LA’ADA WAJE: Abubuwa 10 dangane da sayen Bankin Diamond da Bankin Access ya yi

0

Yau ne aka cimma yarjejeniyar amincewa da sayar da hannayen jarin Diamond Bank ga Access Bank.

A kan haka ne a yau din kuma Access Bank ya hadiye Diamond Bank din, suka cure suka zama daya. Wato maja, irin wacce wasu jam’iyyun siyasa suka yi a cikin 2014, suka hade wuri daya suka kafa APC.

Sakataren bankin kuma Lauya mai maida shawara, Uzoma Uja, ya ce za a kammala maja din bankunan biyu wuri daya nan da tsakiyar shekarar 2019.

PREMIUM TIMES HAUSA ta kawo wasu muhimman batutuwa 10 dangane da cinikin:

1 – Bankin Access ba bako ba ne wajen sayen banki ya narkad da jarin sa a cikin na sa ruwan kudin. Cikin 2012 ya saye Intercontinental Bank. Sai dai kuma an yi zargin ya kori ma’aikatan Intercontinental su 1000. Amma kuma Access Bank ya kara karfi sosai da soasi, tun bayan sayen Intercontinental da ya yi.

2 – Shugaban Bankin Access Herbert Wigwe ya ce hade bankunan biyu zai karfafa samar da dimbin kananan masu zuba jari da kuma habbaka hada-hadar bankin a fadin kasa da kuma Afrika.

3. Access Bank zai zama babban bankin da kananan masu hada-hada za su fi zuba jari a cikin sa a fadin kasar nan.

4 – Hukumomin Diamonda Bank sun ce gaba dayan masu jari, kwastomomi, ma’aikata da masu hada-hada da bankin sun amince cewa hade bankin da Access Bank alheri ne.

5 – Amma fa har yanzu cinikin bai gama fadawa ba tukunna. Akwai wata yarjejeniya ta masu hannayen jari da za a kammala nan ba da dadewa ba, kuma sai an amince da ita tukunna.

6 – Access Bank ya ce ya na da karfinn jari mai tarin yawan gaske, wanda zai kara wa Barno dawakai idan ya hade da Diamond Bank.

7 – Maja din bankunan zai bai wa Access Bank damar mallakar dukkan tsabar kudi, ruwan kudi, uwar kudi da kuma hannayen jarin bankin.

8 – Nan da ranar 13 Ga Disamba, 2018 ce za a yi hada-hadar hannayen jarin Diamond Bank na karshe a Kasuwar Hada-hadar Hannayen Jari ta Najeriya, NSE.

9 – Da an kammala maja din bankunan guda biyu, za a shafe sunan Diamond Bank a doron kasa, a cikin doka da kuma cikin liffafin rakod na sunayen bankunan da ke cin kasuwar hada-hadar hannayen jari ta kasa, wato NSE. A kasuwar hannayen jari ta London ma za a shafe sunan sa, tamkar bai taba bayyana a doron kasa ba.

10 – Za a sake sabon lalen tsarin hada-hadar Bankin Access nan da tsakiyar shekarar 2019.

Share.

game da Author