Hanyoyin guje wa kamuwa da cutar sanyi na ‘Nimoniya’

0

Hanyoyin guje wa kamuwa da cutar hakarkari ‘Pneumonia’

Cutar sanyi dake kama hakarkari ‘Pneumonia’ cuta ce na sanyi dake kama hakarkarin mutum a dalilin shakan gurbataccen isaka da kuma yawan amfani da sanyi.

Bincike ya nuna cewa kwayoyin cuta na ‘Virus, Bacteria da Fungi’ ne ke dasa wannan cutar.

Bincike ya kara nuna cewa cutar na daya daga cikin cututtuka biyar dake kisan yara kanana ‘yan kasa da shekara biyar a duniya.

Sannan an gano cewa a duk shekara cutar kan yi sanadiyyar rayukan yara kananan miliyan 1.2 a duniya.

Alamun wannan sutar sun hada da zazzabi,rashin iya nunfashi yadda ya kamata, ciwon hakarkari,rashin iya cin abinci, suma da sauran su.

Hanyoyin guje wa kamuwa da cutar.

1. Tsaftace muhalli

2. Guje wa shakar gurbataccen iska musamman hayakin risho, itace , bola da sauran su.

3. A daina zama inda ake yawan cinkoso.

4. A daina shaka da zukar taba sigari.

5. Cin abincin dake kara karfin garkuwan jiki musamman ga yara kanana.

6. Yin allurar rigakafin tarin lala, bakon dauro da ciwon hakarkari.

7. Za a iya amfanin da maganin kara karfin garkuwan jiki ‘Antibiotics’ domin kawar da cutar.

8. Iyaye za su iya shayar da ‘ya’yan su ruwan nonon na tsawon shekara daya domin nono na dauke da sinadarorin dake kare yara daga kamuwa da cutar.

9. Iyaye sun kare ‘ya’yan su daga kamuwa da cutar kanjamau.

Share.

game da Author