Hukumar hana yaduwar cututtuka ta kasa (NCDC) ta bayyana cewa a shekarar da muke ciki mutane 143 ne aka rasa a sanadiyyar kamuwa da zazzabin Lassa da suka yi a kasar nan.
Jami’in hukumar Chimezie Anueyiagu ya sanar da haka ranar a tattaunawar da hukumar ta yi da manema labarai a garin a Abuja.
” Bayan gudanar da gwaji mun tabbatar da mutane 559 na dauke da cutar, sannan mutane 143 sun rasu.
Idan ba a manta ba a makon da ya gabata ne Ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya bayyana cewa gwamnati ta fara shirin ganin cutar bata yadu a kasa ba ta hanyar fara shiru tun yanzu da kuma wayar wa mutane kai game da cutar da yadda za su kiyaye kan su.
” A yanzu haka mun horas da m’aikatan da za su wayar wa mutane kai musamman a yankunan karkara.
” Asibitocin mu na ajiye da magungunan kawar da wannan cuta na zazzabin Lassa.
A karshe hukumar hana yaduwar cututtuka ta kasa (NCDC) ta bayyana cewa za ta hada hannu da kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) domin inganta ayyukan su game da cutar.