ZARGIN TAKARDUN JABU: Abin da ya sa ba za mu iya binciken Gwamna Bindow ba – Kakakin Adamawa

0

Kakakin Majalisar Jihar Adamawa, Kabiru Mijinyawa, ya bayyana cewa Majalisar Jihar ba za ta amsa kiran da wata kungiya ta yi mata cewa ta binciki gwamna Bindow ba, bisa zargin mallakar takardar satifiket na jabu ba da ta ce ya yi.

Wata kungiyar fafutika ce mai suna Black Cap Revolution Movement, ta kutsa cikin Majalisar Jihar Adamawa, ta nemi Majalisar ta binciki zargin takardar jabu da ake yi wa gwamnan.

Mijinyawa ya fadi dalilan ne a lokacin da ya ke fada wa sauran mambobi bayanan da ke cikin takardar da kungiyar ta rubuto.

” A ka’idar dokokin majalisa, ba za mu iya tattauna duk wata magana da tuni ta na a gaban kotu ba.”

Bayan wannan kuma, majalisar ta gayyaci Kwamishinar Kiwon Lafiya, Fatima Atiku da sauran jami’an ma’aikatar ta da Akanta Janar ta jihar, Augustina Wandamiya da su bayyana a ranar Alhamis.
An gayyace su ne domin su yi bayanin dalilin rashin biyan albashi har na watanni shida ga wasu sabbin ma’aikatan kiwon lafiya da aka dauka daga baya.

Har ila yau kuma, majalisar ta yanke shawarar nada kwamiti a karkashin Shugaban Masu Rinjaye, Hassan Barguma, dan APC da Karamar Hukumar Hong, domin su binciki yadda aka kashe naira bilyan 2 da Babban Bankin Tarayya ya bayar da sunan lamunin aikin gona ga manoma.

Babban Bankin Tarayya, CBN dai ya ce ya bayar da lamunin ne ta hannun Hukumar Habbaka Hannayen Jari a Jihar Adamawa (AADIL).

Tuni dai dama majalisar ta gayyaci shugaban Hukumar AADIL na jihar, Ibrahim Dasin, wanda a yanzu majalisar ta ce kwamitin bincike ne zai ci gaba da bincikar sa.

Share.

game da Author