Shugaban Jam’iyyar APC, Adams Oshiomhole ya bayyana damuwar sa dangane da artabun sa da jami’an SSS a lokacin da suka gayyace shi aka yi masa tambayoyi kan zargin karbar cuwa-cuwar dagula zabukan fidda-gwani a wasu jihohin kasar nan.
Oshiomhole ya ce ya yi amanna da cewa ba SSS ne suka cancanta su yi masa tambayoyi dangane da zargin harkallar da ake yi masa na karbar cin hanci a lokacin zabukan fidda-gwanin APC ba.
An dai zargi Oshiomhole da karbar kudade masu tarin yawa, inda ya rika baddala sunayen wadanda aka zaba ya na maye gurbin su da na wanda ya shirya daka-daka da su.
A kan haka ne shugaban na APC ya ce, “shin ana ganin ya dace SSS su shiga batun da ya shafi jam’iyyar siyasa?
Idan har akwai zargin cuwa-cuwa a harkar zaben fidda-gwani, to ina ganin aikin EFCC ne da kuma ICPC su yi bincike.” Inji Oshiomhole.
Ya ce karya ne ba a tsare shi a hedikwatar SSS ba, shi ya tuka kan sa ya kai kan sa, kuma shi ya tuka kan sa ya fice da kan sa bayan an kammala yi masa tambayoyi.